IQNA

Masar Ta Kwace Kaddarorin Mutane 1589 Mambobin Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

23:44 - September 12, 2018
Lambar Labari: 3482978
Wani kwamiti da kotun kasar Masar ta kafa ya sanar da kwace kaddarorin mutane 1589 wadanda dukkaninsu mambobi na kungiyar 'yan uwa musulmi

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kwamitin da kotun kasar Masar ta kafa ya kwace kaddarori da dukiyo masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da wasu daga cikin mambobin kungiyar Muslim Brotherhood a kasar.

Daga cikin abubuwa da aka kwace kuwa baya ga dukiyoyi da asusun ajiya a bankuna, akwai kamfanoni 118, kungiyoyi masu gudanar da ayyukan jin kai 1133, makarantu 104, asibitoci 69, tashoshin talabijin da shafukan yanar gizo 33, wadanda dukkaninsu na 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ne, ko kuma wasu mutane masu goyon bayansu a kasar.

A cikin watan janairun farkon shekarar nan ne aka kafa wannan kwamiti a karkashin kotun kasar, wanda yake da hakkin yin bincike da kuma kwace dukiyoyi da kaddarori na 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ko kuma masu goyon bayansu, bisa sabuwar doka mai lamba 22 da amjalisar dokokin kasar ta amince da ita acikin shekara ta 2018.

3746132

 

captcha