IQNA

An Nuna Kwafin Kur’ani Mafi karanta A Duniya A Baje Kolin Littafai Littfai A Jidda

23:57 - January 01, 2019
Lambar Labari: 3483273
Bangaren kasa da kasa, an bude babban baje kolin littafai a birnin Jidda na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa , shafin yada labarai na Alkhaleej ya habarta cewa, a jiya ne aka bude babban baje kolin littafai a birnin Jidda na kasar Saudiyya tare da halartar cibiyoyi da madaba’antu na buga littafai daga sassa na kasar.

A wannan baje kolin littafai an nuna wani kur’ani wanda shi ne mafi karanta a duniya, wanda tsawonsa ya kai 20mm, fadinsa kuma 15mm, sai kuma tudunsa ya kai 8mm.

Abdulllah Bin Hassan Alkinani shi ne shugaban bangaren kula da harkokin al’adu a kasar Saudiyya, ya bayyana cewa wannan baje kolin yana da matukar muhimmanci, domin kuwa shi ne irinsa na farko mafi girma da aka taba gudanarwa a kasar.

Ya ci gaba da cewa, duk da cewa an dauki shekaru hudu ana gudanar da irin wannan baje koli, amma a shekarar bana an samu ci gaba da fuskar yawan littfan da aka kawo nauoi daban-daban wadanda adadinsu ya kai littafi dubu 180.

Haka nan kuma dangane da yadda mutane suka karbi baje kolin, inda a kowace rana daga ranar da aka fara, a kan samu mutane fiye da dubu 50 da suke halartar wurin.

3777496

 

 

 

 

captcha