IQNA

Somalia: Mayakan Al-shabab Sun Kaddamar da Hari kan Sansani MDD

22:54 - January 02, 2019
Lambar Labari: 3483277
Mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab ta kaddamar da hare-hare da makaman roka a kan sansanin majalisar dinin duniya da ke birnin Mogadishu na kasar Somalia.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab ta kaddamar da hare-hare da makaman roka a kan babban sansanin majalisar dinin duniya a kasar Somalia, wanda yake a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Somalia Nicholas Haysom ya bayyana cewa, an kai harin ne a kan bababn ofishin na majalisar dinkin duniya da makaman roka, wanda hakan a cewarsa babban abin bakin ciki ne, domin aikinsu a Somalia shi ne taimaka ma al'ummar kasar.

Ya ce suna yin Allah wadai da wannan hari a kan babban sansanin majalisar dinkin duniya a kasar Somalia, kuma suna fatan kasashen duniya za su dauki matakin kare dukkanin wurare na majalisar duniya da suke a cikin kasar.

Kungiyar Al-shabab ta sanar da cewa ita ce take alhakin kai wannan hari, wanda ya jikakta ma'aikatan majalisar dinkin duniya uku, da kuma yin barna ta kaddarori a wurin.

3777807

 

 

captcha