Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Bawwaba Fito cewa, a yau za a bude bababr majami'a ta mabiya addinin kirista mafi girma ayankin gabas ta tsakiya da gabashin nahiyar Afrika mai suna Milad Masih a kasar Masar.
Wannan majami'a ita ce mafi girma a yankin, kuma shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi da jagoran mabiya addinin kirista na kasar za su jagoranci bude majami'ar.
An gina majami'ar ne a sabon yankin da ka gina domin ayyukan gwamnati a tsakanin birnin Alkahira da kuma mashiga Swis, inda a nan kuma aka gina babban masallacin kasar, inda za a hada masallaci da majami mafi girma ayanki guda domin hada kan mabiya addinain muslucni da kiristanci.
A cikin ginin akwai bangaren da aa ware domin Paparoma, kuma wuri da zai iya daukar mutane 8200 masu ibada.