IQNA

Kotun Sweden Ta Fara Sauraren Shari'ar Wasu Mutane 6 Masu Alaka Da Daesh

23:32 - January 08, 2019
Lambar Labari: 3483295
Bangaren kasa da kasa, a yau kotun kasar kasar Sweden ta fara sauraren shari'ar wasu mutane 6 da ake zargin suna da alaka da kungiyar daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kotun da ke birnin Stocholm fadar mulkin kasar Sweden ta fara zaman nata ne a  yau, inda take zargin mutane da tattara wa kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh kudi da kuma aika su zuwa Syria.

Baya ga haka kuma uku daga cikinsu an samu wasu sanadarai masu guba tare da su, wadanda suka kai nauyin kilo gram 500, kamar yadda kuma aka samu makamai da abubuwan da ake rufe fusaku da su.

Haka na kuma an samu wasu hotuna  a cikin na'urorinsu na kwamfuta da aka dauka a cikin birnin Stocholm, wadanda suka kunshi wasu wurare a cikin birnin, da ake sa ran 'yan ta'addan na niyyar kai hare-hare a kansu.

Biyar daga cikin mutanen 'yan kasar Uzbekistan ne, daya kuma dan kasar Kirgistan ne, amma dukakninsu mazauna kasar ta Sweden ne.

3779374

 

 

 

captcha