IQNA

Yahudawan Isra'ila Sun Keta Alfarmar Wurare Masu Tsarki Sau 100 A Watan da Ya Gabata

22:47 - January 09, 2019
Lambar Labari: 3483299
Minista mai kula da harkokin addini a gwamnatin Palastine ya bayyana cewa, a cikin watan Disamban da ya gabata yahudawan sahyuniya sun keta alfarmar wurare masu tsarki a cikin Palastine har sau 100.

Kamfanin dillancin labaraniqna,  UNA ya bayar da rahoton cewa, a yau laraba minista mai kula da harkokin addini a gwamnatin Palastine Yusud Ad'is ya bayyana cewa, bisa alkalumman da ma'aikatarsa take da su, a cikin watan Disamban da ya gabata yahudawan sahyuniya sun keta alfarmar wurare masu tsarki a cikin Palastine har sau 100 da hakan ya hada da masallacin Quds, da kuma masallacin Annabi Ibrahim da ke garin Alkhalil.

Ya ce yahudawan suna aikata hakan ne da sunan gudanar da tarukan idin yahudawa a cikin watan an Disamba, inda suke kutsa kai a cikin wadannan wurare masu tsarki, tare da keta alfarmarsu.

Ministan ya kara da cewa, dukkanin abin da wadannan yahudawa masu tsatsauran ra'ayi suke aikatawa, suna yin hakan en tare da cikakken goyon bayan gwamnatin Isra'ila, domin kuwa ana basu daruruwan jami'an tsaro da suke ba su kariya a lokacin da suke keta alfarmar wuraren musulmi masu tsarki.

3780068

 

captcha