IQNA

Jehangari Na Ziyarar Aiki A Kasar Syria

23:55 - January 28, 2019
Lambar Labari: 3483336
Mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya kai ziyara kasar Siriya, inda ya samu kyakkyawar tarbe daga Piraministan kasar a birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a marecen wannan Litinin ne mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Ishak Jahangiri ya fara wata ziyarar aiki a birnin Damascus, inda ya samu kyakkyawan tarbe daga Piraministan kasar bayan rera taken jamhoriyar musulinci ta Iran da na kasar Siriya, Jahangiri da Khamis da tawagar dake bayansu sun isa wurin da aka tsara musu liyafa ta musaman.

Bayan kamala liyafar, mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Ishak jahangiri da Piraministan kasar ta Siriya Imad Khamis sun tattauna  a game da canjin da aka samu a yanki, da kuma siyasar Duniya a yankin.

Ana sa ran tawagar da mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ta yi kwanaki biyu a birnin Damuscus, bayan ganawa da shugaban kasar ta Siriya Bashar Asad, Ishak jahangiri tare da tawagarta sa za su halarci taron hadin gwiwa na tattalin arziki tsakanin Iran da Siriya karo na 14.

Har ila yau ana sa ran bangarorin biyu za su sanya hanu kan ci gaba da yarjejjeniyar aiki tare a bangaren tattalin arziki, bayan kamala taron.

3785268

 

captcha