IQNA

MDD Ta Bukaci Bangaladesh Da Ta Gaba Da Daukar bakuncin ‘Yan Kabilar Rohingya

23:39 - March 02, 2019
Lambar Labari: 3483419
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatin kasar Bangaladesh da ta ci gaba da daukar nauyin bakuncin ‘yan gudun hijirar Rohingya zuwa wani lokaci.

Kafanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancinlabaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya Shahidul Haq ministan harkokin wajen kasar bangaladesh ya sanar damajalisar dinkin duniya cewa, kasarsa ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin ci gaba da kula da ‘yan gudun hijirar Rohingya ba.

A nasa bangaren kakain majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric ya bayyana cewa, majalisar dinkin duniya tana  bukatar gwamnatin kasar Bangaladesh da ta ci gaba da daukar nauyin bakuncin ‘yan gudun hijirar Rohingya zuwa wani lokacia nan gaba kafin warware matsalarsu domin komawa kasarsu.

Wannan ya zo ne kwanaki biyu bayan rahoton da babbar jami’ar majlaisar dinkin duniya kan rikciin Myanmar ta mika ga kwamitin tsaron majalisar, wanda yake nuni da cewa musulmi ‘yan kabilar Rohingya ‘yan kasar Myanmar da suke gudun hijira  a kasar Bangaladesh suna cikin mawuyacin hali.

Yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijirar Rohingya sama da dubu 750 a kasar Bangaladesh a sansanonin da aka tsugunnar da su.

3794543

 

 

 

captcha