IQNA

Trump Ya Yarda Cewa Ba Su Iya Cimma Manufofinsu A Syria Da Iraki Ba

23:48 - March 03, 2019
Lambar Labari: 3483420
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ba cimma komai a Syria da Iraki da ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani dogon jawabi da ya gabatar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ikirari da bakinsa cewa ba cimma manufofinsu a Syria da Iraki da ba.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman da ya yia  ‘yan lokutan baya, inda yake cewa sun kaya lagon Daesh a Syria da Iraki, a kan za su janye dakarunsu daga Syria, wanda hakan ke warware maganarsa ta farko.

A cikin shekara ta 2017 Trump ya bayyana cewa, sun kasha fiye da dala biliyan 700 a yankin gabas ta tsakiya, amma babu wata riba ta a zo a gani da suka samu, a kan dole ne kawayensu na yankin musamman saudiyya su fitar da kudi matukar suna son Amurka ta ci gaba da ba su kariya.

Haka nan kuma Trump yay i kakkausar suka kan tsohon sakataren tsaron Amurka James Mattis wanda suka raba gari da shi, inda y ace Mattis ya cika sanyin jiki wajen yaki da ‘yan ta’adda.

3794893

 

 

captcha