Kamfanin dillanciuin labaran iqna , kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta soki siyasar kasarta kan shigar shugula acikin harkokin Venezuela na cikin gida.
Ta ce yanayin da Venezuela take ciki ba yanayi mai kyau ba, kuma siyasar da gwamnatin Amurka ta dauka wajen kara ruruta wutar rikici a kasar ba a bu ne da ya dace ba, maimakon haka hanyar hada kan al’ummar kasar domin warware matsalolinsu ta hanyar tattaunawa ita kadai ce mafita.
A nasa bangaren Mike Pence mataimakin shugaban Amurka, ya zargi Ilhan Omar ta fita tsarin gurguzua kan tsarin Demukradiya, saboda taki amincewa da siyasar haddasa husuma da rikici da gwamnatin Amurka ta dauka a kan kasar Venezuela.