IQNA

Isra'ila Ta Kara Rage Yawan Yankunan Ruwa Da Falastinawa Ke Kamun Kifi

23:56 - June 06, 2019
Lambar Labari: 3483716
Bangaren kasa da kasa, Isra’ila ta sak rage fadin ruwan da falastinawa suke gudanar da sana’ar kamun kifi a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Zakariyya Bakr shugaban kungiyar masu kamun kifi a yankin zirin Gaza ya sanar yau cewa, Isra’ila ta sanar da cewa daga yanzu Falastinawa na hakkin kamun kifi ne kawai a tsawon ruwa da bai wuce mil 10 ba.

Ya ce wannan matakin an dauke shi ne kan falastinawa masu yin sanar kamun kifi a cikin ruwan da ke gabar zirin Gaza.

A yarjejeniyar Oslo, an amince kan cewa falastinawa zirin gaza suna da hakkin gudanar da dukkanin harkokinsu a cikin ruwa har tsawon mil 20, amma daga bisani Isala ta mayar ad shi mil 15,a  yau kuma ta mayar da shi mil 10, kuma akwai yiwuwar ta ci gaba da kara rage yawan fadi da tsawon ruwan wanda falastinawa suke samun gudanar da harkokin musamman sana’ar kamun kifi a  cikinsa.

 

3817407

http://iqna.ir/fa/news/3817407

captcha