Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Muhammad said wani musulmi mai fafutuka akasar Afrika ta kudu, ya bayyana cewa shirin da gwamnatin saudoyya take da shi na shirya wani taro na wakoki da raye-raye a ranar 18 ga Yuli da hakan babban cin fuska ne ga dukkanin musulmin duniya.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatin saudiyya ta shirya wannan babban taron raye-raye da badala ne a daidai lokacin tuni maniyyata musulmi daga dukkanin kasashen duniya suka fara isa kasar domin gudanar da aikin hajji.
Baya ga haka kuma wannan wata wata ne mai alfarma na zulkida wanda wata ne da ake lissafa shi a matsayin watan shirin aikin hajji, wanda tozarta wannan wata yana matsayin tozarta aikin hajji, da ma alhazai da suke isa kasar a halin yanzu.
Yariman saudiyya ya shirya wannan taron kide-kide da raye-raye ne da sunan yana son jawo hankulan masu saka hannayen jari daga kasashen waje musamamn na turawa.