IQNA

Mutane Dubu 140 Ne Suka mutu Ko Jikkata A Hare-Haren Saudiyya A Yemen

23:52 - August 30, 2019
Lambar Labari: 3484000
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Yemen ta sanar da cewa, akalla mutane dubu 140 ne tsakanin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka samu raunuka a kasar, sakamakon hare-haren Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Alamsirah ta kasar Yemen cewa, Taha Mutawakkil ministan kiwon lafiya na gwamnatin hadin kan kasa da ke da mazauni a San’a ya bayyana cewa, bisa kididdigar da suka gudanar sun iya gano cewa, kimanin mutane dubu 140 tsakanin wadanda suka mutu da wadanda suka samu munanan raunuka sakamakon hare-haren jiragen yakin Saudiyya a kan al’ummar kasar Yemen.

Ya ci gaba da cewa; daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare a cikin shekaru sama da hudu da suka gabata ya zuwa, ta rusa cibiyoyin kiwon lafiya kimanin 700 a fadin kasar Yemen.

Ya kara da cewa a halin yanzu akwai dakunan ayyukan tiyata a asibitoci 25 a birnin San’a da suka daina aiki, saboda rashin kayan aiki ko kuma saboda hare-haren saudiyya sun shafe su.

3838388

 

 

 

captcha