IQNA

Ministan Tsaron Iraki: Ba Za Mu Amice Da Kaiwa Kasarmu Hari Ba

23:44 - August 31, 2019
Lambar Labari: 3484004
Bangaren kasa da kasa, Ministan tsaron kasar Iraqi ya bayyana cewa za su dauki matakan soja domin kare kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ministan tsaron kasar Iraqi Najah al-Shimmari ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; Za kuma su dauki matakan soja domin kare kasar Iraki.

Al-shimmari wanda ya fitar da bayani bayan da ya halarci taron gaggawa da majalisar tsaron kasar ta Iraki ta yi, ya kuma ce; Wajibi ne a kasance a cikin fadaka domin hana taba hurumin kasar Iraki da wasu kasashen za su yi.

Taron majalisar tsaron kasar ta Iraki ya sami halartar babban hafasan hafsoshin sojan kasar da mataimakansa, da kuma manyan kwamandojijin sojan kasar ta Iraki.

Ministan tsaron kasar ta Iraki ya yi kira ga dukkanin bangarorin soja da ‘yan sandan da dakarun sa kai na Hashdus-sha’abi da Psihmarga, da su hada kai domin kalubalantar duk wanda yake son cutar da tsaron kasar Iraki.

Makwanni biyu da su ka gabata ne dai haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari da jirgi maras matuki akan wani sansanin dakarun sa kai na Hashdus-sha’abi, wanda ya yi sanadiyyar shahadar wasu daga cikinsu.

 

3838778

 

 

captcha