Kamfanin dillancin labaran iqna, rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda sun amfani da karfi domin tarwatsa mambobin Harkar Musulunci da suke gudanar da jerin gwanon ashura a birane daban-daban.
Rahotannin sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da harsasan bindiga, inda suka kashe mutane 3 a garin Kaduna tare da jikkata wasu.
Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye a wasu garuruwan domin tarwatsawa mabiya Harkar musulunci da suke gudanar da jerin gwanon Ashura, yayin da kuma a wasu biranan an yi tarukan lami lafiya ba tare da jami’an tsaro sun taba wani ba.