IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Zama Kan Batun Palestine

22:58 - September 11, 2019
Lambar Labari: 3484040
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi tana shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun yunkurin Isra’ila na hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, gwamnatin Saudiyya ta kirayi zaman gaggawa na kungiyar kasashen musulmi dangane ad yunkurin Isra’ila na hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Wannan mataki na saudiyya na zuwa ne bayan barazanar da firayi ministan Isra’ila ya yi ne kan cewa idan ya lashe zabe mai zuwa wanda za a gudanar a ranar 17 ga wannan wata na Satumba, zai hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan da sauran yankunan Isra’ila.

Wannan furuci dai yana ci gaba da fuskantar martani daga ko’ina cikin fadin duniya, da hakan ya hada har daga manyan kawayen Isra’ila daga cikin kasashen larabawa.

A cikin yankunan falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan dai a halin yanzu akwai matsugunnan yahudawa guda 250, inda yahudawa dubu 400 suke zaune a cikinsu.

3841556

 

  

 

 

captcha