Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wuto cewa shekh Muhammad Abdulkadir babban limamin masallacin Safa a cikin jahar Qana a kasar masar ya bayyana ranar Arafah da cewa rana ce ta bayyana karfin addinin muslunci da kuma bayyana shi ga sauran al'ummomin duniya.
Malamin ya ci gaba da cewa ko shakka babu lamarin aikin hajj yana tatatre da hikimomi na ubangiji da suke daga addinin muslunci a kowace shekara tare da bayyana karfinsa da kuma karfin al'ummar musulmi ga sauran al'ummomin duniya, da kuma yadda hakan kan yi tasiri wajen hada kan al'ummar musulmi waje guda a cikin lamarinsu.
Ya kara da cewa matukar dai musulmi suna son su samu wadannan falaloli da kuma daukaka daga ubangiji sai sun yi amfani da wadannan ayyuka na ibadar ubangiji kamar yadda Allah ya umarta tare da kiyaye dukaknin ladubba da ke kunshe a cikin wadannan ayyuka masu albarka, idan har musulmi suka yi to kuwa za su ga wannan faida da Allah ya sanya a aikin hajji da sauran ayyuka na ibada baki daya.
Babbar manufar haji dai ita ce misltuwa da umarnin ubangiji kan ayyukan da ke ciki, sa'annan kuma babbar manufar siyasa it ace hada musulmi domin sanin halin da suke daga koina da kuma karbar umarni na bai daya amatsayinsu na al'umma guda.