Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo muslim walch cewa, Abdulrahamn Al-sudais shugaban hukumar kula da ayyukan harami a Saudiyya ya tabbatar da cewa a ranar Arafah ne za a gudanar ada aikin canja kyallen da ke kan dakin ka’abah mai alfarma kamar dai yadda aka saba.
Jami’in ya ci gaba da cewa ana yin wannan aiki a kowace shekara a tsawon tarihi, kuma a kan dunka wannan kya;lle a kasar Masar da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi, kuma a kan wanke dakin ka’abah da ruwan furanni daga birnin Kashan na kasar Iran, wanda kuma hakan yana daga cikin abin da ake yi tun tsawon daruruwan shekaru.
A kan wannan kyalle dai ana rubuta ayoyin kir’ani mai tsarki nay abo da girmama ga matsayin ubangiji madaukakin sarki, haka nan kuma a kan rubuta sunayen ubangiji masu tsarki a dukkanin bangarori na wannan kyalle, bayan duba shi da kuma tabbatar da cewa dukkanin abubuwan da aka rubuta a kansa da suka hada ayoyin kur’ani da sunayen ubangiji daidai suke ba tare da wani kure ba, to daga nan za a mika shi ga hukumar da ke kula da haramin mai tsarki, wadda it ace za ta sanar da ranar saka a shi a kandakin mai albarka.
1454795