IQNA

Sakon Jagora ga Mahajjata Na Bana

16:40 - November 15, 2010
Lambar Labari: 2032718
Wannan Fassarar sakon jagoran juyin juya halin musulunci ne a cikin harshen ahusa.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga
Muhammad Mustafa da alayensa tsarkaka da sahabbansa zavavvu
Ka’aba alama ce ta haxin kai, xaukaka da kuma tauhidi da tsarkin zuciya, a lokacin
aikin hajji zukata masu bege da kyakkyawan fata da suka zo daga kowane vangare na
duniya domin su amsa kiran ubangiji maxuakaki suna masu cewa mun amsa kiranka
“Labbaika” suna masu sauri zuwa ga matsirar addinin musulunci. Al’ummar musulmi
a yau zasu iya ganin sura dunqulalliya ta yaxuwar, canje-canje da zurfin imani wanda
ya mamaye zukatan mabiya wannan addinin na musulunci, ta hanyar wakilansu
(alhazai) waxanda suka tattaru daga kusurwowi huxu na duniya, kuma su san wannan
babban jari wanda babu irinsa.
Wannan wani lamari ne da zai taimaka wa al’ummar musulmi su qara sanin
kawukansu a yau da kuma gobe, kuma su fara motsawa zuwa ga tabbatuwar hakan.
Yaxuwar farkawar nan ta musulunci a duniyar yau wani tabbaci ne da yake yin
albishir na alheri ga al’ummar musulmi. Wannan motsi ya fara ne daga shekaru
talatin da suka wuce daga lokacin cin nasarar juyin musulunci da kuma kafuwar
tsarin musulunci a Iran. Babbar al’ummarmu ba tare da wani tsaiko ba ta samu ci
gaba, kuma ta kawar da shingayen da suka sha gabanta, ta samu cin nasara a fagage
daban-daban. Saboda ci gaban da al’ummar musulmi ta yi ne maqiya suka xauki salo
murxaxxe da qoqari baji-bagani ta hanyar kashe kuxaxe masu yawan gaske wurin
yaqi da addinin musulunci. Yaxa mummunar farfaganda domin qyamar musulunci,
da qoqarin samar da savani tsakanin vangarorin musulmi, da ingiza vangarancin
mazhabobi, kamar qirqirar qarya don qyamar shi’a wa mabiya sunna, da qirqirar
gabar sunna ta qarya ga yan shi’a, jefa savani tsakanin qasashen musulmi, da qoqarin
tsananta savani da mayar da shi qiyayya, ko wani shu’umin lamari mai wuyar
warwara, da kuma amfani da qungiyoyin leqen asiri wurin yaxa varna da alfasha
tsakanin samari, dukkanin wannan ba domin komai ba, sai don a kawar da motsin nan
mai qarfi da tsayuwar al’umma qyam zuwa ga farkawa, xaukaka, da ‘yanci.
Haramtaccen tsarin sahyoniyanci a yau savanin shekara talatin da suka wuce, ba wani
babban dodo ba ne wanda ba za a iya rusa shi ba. Haka nan savanin shekaru ashirin
da suka wuce Amurka da qasashen turai ba su ne masu yanke shawarar da ba a iya
cewa uffan ba a kan yankin gabas ta tsakiya. Sannan har yanzu savanin shekaru goma
da suka wuce, fasahar nukiliya da sauran fasahohi masu zurfi, ba a ganin wasu
abubuwa ne da suke da wahalar samu ga al’ummar musulmi da mutanen gabas ta
tsakiya. A yau al’ummar Falasxinu gwarazan gwagwarmaya ne, al’ummar Lebanon
su kaxai suka karya kwarjinin da ake gani na tsarin sahayoniyanci, kuma su suka ci
nasara a yaqin kwana 33; kuma al’ummar Iran su ne baraden da suka yi fice a wajen
buxe sababbin shafukan ci gaba .
A yau Amurka mai girman kai ta sanya kanta a matsayin xan sandan qasashen
musulmi, kuma babban mai bayar da xaurin gindi ga haramtaccen tsarin
sahayoniyanci, ta maqale cikin matsalolin da ta haifar a Afganistan, kuma a Iraqi duk
da ta’addancin da ta yi sai ga shi tana komawa gefe, kuma ta zama abar qyama a
qasar Pakistan da ta faxa cikin wahala. A yau rundunar yaqi da addinin musulunci da
ta kasance tana mulkin al’umma da hukumomi ta hanyar danniya ga al’ummar
musulmi na tsawon qarni biyu, tana kuma kwashe albarkatunsu, sai ga shi tana ganin
gushewar tasirinta, da tsayawar musulmi da jarumta qyam a gaban wannan runduna.
Ta xaya vangaren kuma farkawar musulunci tana qara yaxuwa, dole ne wannan
yanayi mai bayar da qwarin gwiwa, kuma wanda yake xauke da albishir, ya zama ya
ciyar da al’ummar musulmi gaba, ta wani vangaren kuma ya sanya su mafi kaifin
basira ta hanyar xaukar darussa da abubuwan lura. Wannan saqon babu shakka zai
sanya malaman addini da shugabannin siyasa da qwararru da matasa jin xaukar
nauyin sa fiye da kowa. Yana kuma neman su yi matuqar qwazo.
Kur’ani mai girma yana yi mana bayani a fili cewa: “Kun kasance mafificiyar
al’umma da aka fitar domin mutane, kuna umarni da kyakkyawa kuma kuna hani ga
mummuna, kuma kuna masu imani da Allah”. A bayanin wannan ayar dalili kuma
babbar manufa shi ne samar da al’ummar musulmi maxaukakiya domin samun tsira
da alheri ga xan Adam.
Babban nauyin da ya hau kan al’umma shi ne umarni da kyakkyawa, da hani ga
mummuna, da imani da Allah. Babu wani kyakkyawan aiki da ya fi tsiran al’umma
daga hannun ‘yan kama karya, kuma babu mummunan aikin da ya fi xamfaruwa da
azzalumai ‘yan danniya. A yau babban nauyin da ya hau kan jagorori da shugabannin
al’umma shi ne; taimaka wa al’ummar Falasxinawa, da waxanda aka qaqaba wa
takunkumi a Gaza, da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Pakistan, Afganistan,
Iraqi, da Kashmir, qoqarin tsayuwa gaban ta’addancin Amurka da haramtacciyyar
daular sahayoniyanci. Sai kuma kiyaye haxin kai tsakanin al’ummar musulmi, da
fito-nafito da gurvatattun hannaye da harsunan ‘yan barandan da suke hana haxin kan
al’umma, da kuma yaxa farkawa da jin xaukar nauyi a tsakanin matasan musulmi a
kowane vangare na musulunci.
Aikin hajji wata dama ce wacce za a yi amfani da ita wajen aikata waxannan
abubuwan da aka ambata, kuma yake kiran mu zuwa ga ninka himma da ninka
qwazo.
Assalamu Alaikum
Sayyid Ali Husaini Khamna’i
Xaya ga Zulhajji 1431
8 -11- 2010
captcha