IQNA

Gwagwarmayar Musulunci A Lebanon Ta Samo Asali Ne Daga Tunanin Waki’ar Karbala

17:22 - December 05, 2011
Lambar Labari: 2234380
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, sadaukantarwar da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzon Allah suka yi a Karbala, na da babban tasiri wajen kafuwar gwagwarmaya da zalunci a kasar Lebanon.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, sadaukantarwar da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzon Allah suka yi a Karbala, na da babban tasiri wajen kafuwar gwagwarmaya da zalunci a kasar Lebanon daga ciki kuwa har da kungiyar ta Hizbullah.
Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubabn mutane da suka taru a hubbaren Sayyid Abbas Musawi, wanda shi ne sakataren kungiyar ta Hizbullah da ya yi shahada sakamakon harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kansa tare da iyalansa a lokacin da suke tafiya a mota.
Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, sadaukantarwar da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzon Allah suka yi a Karbala, na da babban tasiri wajen kafuwar gwagwarmaya da zalunci a kasar.
910516


captcha