Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da wani jawabi dangane da makon tunawa da shahidan gwagwarmayar Lebanon da kuma batutuwa da suka shafi siyasar yankin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alaman cewa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon zai gabatar da wani jawabi dangane da makon tunawa da shahidan gwagwarmayar Lebanon da kuma batutuwa da suka shafi siyasar yankin baki daya da kuma dasisar makiya suke kullawa.
Daga cikin muhimamn a bubuwan da jawabin nasa zai mayar da hankali kansa hard a shahadar Sayyid Abbas Musawi tsohon sakataren kungiyar ta hizbullah, da kuma shekh Ragib Harb wanda shi ma ya yi shahada ne a hannun haramtacciyar kasar Isra'ila, a lokacin da suka harba bam a gidansa.
Bayanan kuma Sayyid zai tabo batutuwa da suka danganci halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya baki daya, da kuma abubuwan da ake shirwa yankin na makirci daga makiya, wanda wasu daga cikin gwamnatocin yankin ne suke aiwatar da wannan siyasa domin cutar da musulmi.
959307