IQNA

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1433-2012)

15:27 - October 27, 2012
Lambar Labari: 2438566
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzo mafi girma tare da Alayensa tsarkaka da zababbun sahabbansa.


Lokacin aikin hajji, wanda lokaci ne da ke cike da rahama da albarkoki, ya iso sannan kuma a wannan karon ma Allah Madaukakin Sarki ya gabatar da wannan sa’adar da ake samu a wannan lokaci mai haske. Wannan wajen da kuma wannan lokacin suna kiranku, Ya ku mahajjata, zuwa ga daukaka yanayinku na duniya da lahira. A wajen nan ne maza da mata musulmi, da zuciya da kuma harsunansu, suke amsa kiran Allah Madaukakin Sarki zuwa ga ababen da za su amfane su da kuma samun tsira. Nan waje ne da ya ke ba wa kowa da kowa damar jarraba mu’amala ta ‘yan’uwantaka da kuma tsoron Allah. Wannan waje, wani sansani ne na tarbiyya da koyo; waje ne na bayyanar da hadin kai da daukaka da kuma tabbatar da cewa al’ummar musulmi guda ne duk kuwa da bambanci na kabila da launin fata da suke da shi; sannan kuma waje ne na fada da Shaidan da dagutu. Wannan waje ne da Allah Madaukakin Sarki Ya sanya shi a matsayin wajen da muminai za su shaidi abubuwa masu amfani a gare su. A lokacin da muka bude idanuwan mu na hikima da daukan darasi, to kuwa wannan alkawari na Ubangiji zai ba mu damar koyon dukkanin abubuwan da suke cikin rayuwa ta daidaiku da kuma ta jama’ance. Kebantattun siffofin da suke cikin ayyukan hajji suna hada rayuwar duniya da ta lahira haka nan kuma da rayuwa ta daidaiku da ta al’umma. Dakin Ka’aba madaukaki; yin dawafi da jiki da zukata yayin zagaya wannan madaukakin wajen; sa’ayi da kokari ba dakatawa kuma cikin tsari (da ake yi) tsakanin wani mafari da kuma inda ake karkarewa; haka nan irin wannan hijira ta gaba daya zuwa ga sansanin (da ke tunawa mutum) ranar Kiyama a Arafa da Mash’ar da irin halarta ta zuciya da ake samu a wannan taro mai girma; hakan nan hari na gaba daya da ake kai alama ta Shaidan; da kuma wannan taruwa ta gaba daya daga dukkanin bangarori na duniya sannan kuma daga dukkanin al’ummu ma’abota launuka da yarurruka mabambanta a lokacin wannan biki da ke cike da abubuwa masu kusata mutum da Ubangiji kana kuma alama ta shiriya….dukkanin wadannan siffofi ne marasa tamka da wannan farilla da ke cike da ma’ana da ababe masu amfani ya kebanta da su.

Irin wannan bikin ne yake iya hada zukata cikin ambaton Allah sannan kuma ya ke haskaka zukatan mutane da haske na tsoron Allah da kuma imani. Haka nan kuma shi ne ya ke fitar da mutum daga shamakin da ya sanya wa kansa da kuma sanya shi cikin gungun al’ummar musulmi; haka nan kuma ya kan sanya masa tufafin tsoron Allah da ke kare ransa daga dauda ta zunubi, haka nan kuma ya kan ba shi ruhi da karfin gwuiwa na tinkarar shaidanu da dawagitai. A irin wannan wajen ne alhaji yake iya ganin girman da al’ummar musulmi suke da shi da idanuwansa da kuma ganin irin karfin da suke da shi sannan kuma hakan ya kan kara masa kyakkyawan fata ga makoma da ya ke da shi; kamar yadda kuma hakan ya kan ba shi damar yin shiri wajen taka gagarumar rawa a wannan fagen; haka nan kuma idan har ya samu dacewa da kuma taimako na Ubangiji ya sake yin mubaya’a ga Manzon Allah da kuma addinin Musulunci mai girma da kuma sama wa kansa wata azama mai girma ta gyara kansa da kuma al’umma da kuma daukakar kalmar Musulunci.

Dukkanin wadannan abubuwa guda biyu, wato gyara kai da kuma gyaran al’umma, wadansu farillai ne guda biyu da ba za a taba yin watsi da su ba. Tabbatar da hakan ta hanyar tuntuni cikin ayyuka na addini da kuma amfani da hikima da basira ba wani lamari ne mai wahalar gaske a wajen ma’abota tunani ba.

Gyaran kai ya kan faro ne daga fada da waswasi na shaidan da kuma kokari wajen nesantar zunubai, sannan gyaran al’umma kuma yana farawa ne daga fahimtar makiyi da makirce-makircensa da kuma kokari wajen rage kaifin cutarwarsa da yaudara da kuma kiyayyarsa, bayan an samu hakan kuma sai a hada da karfi na hadin kai da al’ummar musulmi suke da shi.

A halin yanzu, daya daga cikin lamurra masu muhimmancin gaske da suka shafi duniyar musulmi wanda kuma yake da alaka da makomar al’ummar musulmin shi ne juyin juya halin da ke faruwa a kasashen arewacin Afirka da kuma Jazirar larabawa wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar faduwar wasu lalatattun gwamnatoci ‘yan amshin shatan Amurka kuma kawayen sahyoniyawa kamar yadda kuma ya jijjiga wasu gwamnatoci makamantan wadancan. Matukar dai al’ummar musulmi suka bari wannan dama ta kubuce musu sannan kuma ba su amfana da hakan ba wajen gyaran al’ummar musulmi, to kuwa lalle sun yi babbar hasara. A halin yanzu dai ma’abota girman kai masu wuce gona da iri da tsoma baki cikin lamuran wadansu suna ta amfani da dukkan karfinsu wajen karkatar da wannan gagarumin yunkuri na Musulunci.

A yayin wannan gagarumin yunkuri dai, musulmi maza da mata sun mike da yunkurawa ne wajen kawar da kama-karyar shugabanni da mulkin mallakan Amurka wacce take kaskantar da al’ummomi sannan kuma da hada baki da ‘yar ta’addar gwamnatin sahyoniyawa. Masu wannan yunkurin dai sun riki Musulunci da koyarwarsa a matsayin abin da zai ‘yantar da su, sannan kuma a fili suke sanar da hakan. Haka nan kuma sun sanya goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma fada da haramtacciyar gwamnatin ‘yan fashi (ta sahyoniyawa) a matsayin manyan manufofi da bukatunsu. Sun mika hannayen abokantaka ga al’ummomin musulmi na duniya su na masu fatan ganin an samu hadin kai tsakanin al’ummar musulmi.

Wadannan su ne tushen wadannan yunkuri na al’umma da suka faru a kasashen da cikin shekaru biyun da suka gabata aka daga tutar neman ‘yanci da gyara a cikinsu sannan kuma jama’a suka shigo fagen juyin juya juya hali suna masu sadaukar da rayukansu; wadannan abubuwan kuwa su ne za su iya tabbatar da tushe na asasi na gyara cikin al’ummar musulmi masu girma. Ko shakka babu sharadin samun nasara ta gaba daya cikin wadannan yunkuri na al’umma shi ne tsayin daka wajen riko da wadannan tushen.

To sai dai makiya suna ta kokari wajen ganin sun raunana wadannan tushe na asalin. Lalatattun hannayen Amurka da kungiyar NATO da sahyoniyawa ta hanyar amfani da wasu gafalallu da masu kananan kwakwalwa suna ta kokarin karkatar da wannan gagarumin yunkuri na matasa musulmi, sannan kuma su hada su fada da junansu da sunan Musulunci haka nan kuma su mayar da jihadin tinkarar ‘yan mulkin mallaka da kuma sahyoniyanci zuwa ga ayyukan ta’addanci a lunguna da titunan kasashen musulmi don musulmi su da kansu su dinga zubar da jinin junansu su kuwa makiyan Musulunci su tseratar da kansu daga tsaka mai wuyan da suke ciki kana kuma su bakanta sunan Musulunci da jihadinsa.

Sakamakon yanke kaunar da (makiyan) suka yi daga kawar da Musulunci da takensa (daga zukatan al’ummomi), a halin yanzu sun koma ga kokarin haifar da fitina a tsakanin kungiyoyin musulmi sannan kuma ta hanyar shigo da makircin sanya kyamar ‘yan Shi’a (cikin zukatan ‘yan Sunna) da kyamar ‘yan Sunna (cikin zukatan ‘yan Shi’a), suna son cutar da hadin kan da musulm suke da shi.

Wadannan mutanen ta hanyar amfani da ‘yan amshin shatansu na yankin nan, sun haifar da rikici a kasar Siriya don su kawar da kwakwalan al’ummomi daga batutuwa masu muhimmanci na kasashensu da kuma hatsarin da ke fuskantarsu da kuma sanya su cikin wannan yanayi na zubar da jini wadanda su da kansu ne suka kirkiro shi. Yakin basasa da yadda matasa musulmi suke zubar da jinin junansu, wani danyen aiki ne da Amurka da sahyoniyawa da kuma gwamnatoci ‘yan amshin shatansu suka faro shi sannan kuma suke ci gaba da ruruta wutar hakan. Waye zai gaskata cewa gwamnatocin da suke goyon bayan bakaken ‘yan mulkin kama-karya a kasashen Masar da Tunusiya da Libiya, to amma a halin yanzu kuma sun zamanto masu goyon bayan tabbatar da demokradiyya a kasar Siriya? Abin da ke faruwa a kasar Siriya, wani daukar fansa ne a kan gwamnatin da shekaru talatin kenan ita kadai din ta ta tsaya kyam a gaban sahyoniyawa ‘yan fashi, kana take ba da kariya da kuma goyon baya ga kungiyoyin gwagwarmaya a Palastinu da Labanon.

Mu dai muna goyon bayan al’ummar Siriya amma kuma muna adawa da duk wata tunzurawa da kuma tsoma baki na kasashen waje cikin wannan kasar. Duk wani gyaran da za a yi a wannan kasar wajibi ne ya kasance ta hannun al’ummar kasar sannan kuma ta hanyar wacce take ta al’umma ce. Irin yadda ‘yan mulkin mallaka na kasa da kasa bisa taimakon gwamnatoci ‘yan amshin shatansu na wannan yankin suka haifar da fitina a wannan kasar (ta Siriya) sannan kuma ta hanyar fakewa da batun rikicin su share wa kansu fagen aikata duk wani nau'i na munanan ayyukan, lalle hakan wani hatsari ne mai girman gaske wanda matukar dai gwamnatocin wannan yankin ba su yi maganin hakan ba, to su zauna cikin shirin zuwan na su lokacin da za su fada cikin wannan tarko na makirci na ma’abota girman kai.

Ya ku ‘yan’uwa maza da mata! Lokacin aikin hajji wata dama ce ta yin tunani mai zurfin gaske cikin lamurra masu muhimmanci na duniyar musulmi. Daga cikin wadannan lamurra masu muhimmancin kuwa har da makomar wadannan juyin juya hali da suke faruwa a yankin nan da kuma kokarin da ma’abota girman kai da suka sha kashi a hannun wadannan juyin suke yi wajen karkatar da wannan juyin daga tafarkinsa. Ha’incin da wasu suke yi wajen haifar da sabani tsakanin musulmi da haifar da mummunan zato da rikici tsakanin wadannan kasashen da aka yi juyi da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran; batun Palastinu da kuma kokari wajen mayar da ‘yan gwagwarmaya saniyar ware da kuma kashe wutar gwagwarmayar Palastinawa; farfagandar nuna kiyaya ga Musulunci da gwamnatocin kasashen yammaci suke yi da kuma nuna goyon bayansu ga masu cin mutimcin Manzon Allah (s.a.w.a); share fagen yakin basasa da rarraba wasu kasashen musulmi, tsoratar da gwamnatoci da al’ummomi ma’abota juyin juya hali dangane da nuna kiyayya ga ‘yan mulkin mallaka na kasashen yammaci da kuma yada cewa makomarsu tana cikin mika kai ne ga wadannan masu wuce gona da irin…..da sauran batutuwa masu muhimmanci makamantan wadannan, suna daga cikin lamurra masu muhimmanci da wajibi ne a yi tuntuni cikinsu a lokacin aikin Hajji sannan kuma karkashin inuwar irin wannan so da kauna da kuke nunawa, Ya ku mahajjata.

Ko shakka babu shiriya da kuma taimako na Ubangiji za su share wa mumimai masu kokari hanyar samun aminci da kwanciyar hankali: “Kuma wadannan da suka yi kokari wajen neman yardarmu, Lalle za mu shiryar da su zuwa ga hanyoyinmu….” (Suratul Ankabut 29:69)

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Sayyid Ali Khamenei
30, ga watan Mehr, 1391.
5 ga watan Zul Hajji 1433.
21, ga watan Oktoba, 2012.


1126513
captcha