Kamfanin dillancin labaran quran na Iqna ya nakalto daga shafin jagoran cewa, Ayatollah Ozma sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gudanar da gagarumin zabe a matsayin wata garkuwa ta tabbatar da tsaron kasar Iran da kuma kawar da barazanar da kasar take fuskanta daga makiya inda ya ce: Tsarin Jamhuriyar ta Iran, wani tsayayyen tsari ne da ya kafu da kafafunsa, wadanda mutane su ne wadannan kafafun.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin goyon bayan da mutane suke ba wa tsarin Musulunci a matsayin abin alfahari da kuma albarka ga kasa, tsarin Musulunci da kuma su kansu mutane, daga nan sai ya ce: Bisa la'akari da cewa zabe wata alama ce ta fitowa da kasantuwar mutane a fage, don haka wajibi ne a gudanar da gagarumin zaben da mutane za su fito kwansu da kwarkwatarsu.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da dokoki masu kyau na zabe da ake da su a Iran, Jagoran cewa ya yi: Ya zuwa yanzu dai dukkanin abubuwan da aka gudanar suna tafiya ne bisa doka sannan kuma ‘yan takaran da suka gabatar da sunayensu cikin tattaunawar da suke yi da manema labarai sun bayyana aniyarsu ta girmama doka shi din ma bayan an sanar da sunayen ‘yan takaran da aka tantance sunayensu ne. A saboda haka wajibi ne a nuna godiya da kuma jinjinawa dukkanin ‘yan takaran musamman wadanda ba a tantance sunayensu ba.
Jagoran ya bayyana hakan a matsayin abin da ke tabbatar da muhimmancin da doka take da shi kenan inda ya ce: Mai yiyuwa ne ya zamanto wata dokar ba ta yi mana dadi ba, to amma mika wuyanmu ga doka abu ne da ke tabbatar da cewa doka dai ita ce a kan gaba.
Batu nag aba da Jagoran ya yi magana kansa shi ne batun fahimta, taka tsantsan da kuma sanya basira cikin zaban dan takaran da ya dace a lokacin zaben inda ya ce: sakamakon irin fahimtar da mutanen Iran suke da ita dangane da lamurran da suka shafi siyasa, haka nan kuma da irin fagen da hukumar gidan radiyo da talabijin ta samar (na ba wa ‘yan takaran damar yin yakin neman zabe), don haka ana iya cewa an samar da yanayin da mutane za su iya zaban dan takaran da suka ga ya dace.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne mutum ya yi daidai ko kuma ya yi kuskure wajen zaben mutumin da ya dace, babu matsala cikin hakan. Abin da ke da muhimmanci shi ne ya zamanto ya yi aiki da sakamakon da ya cimma ne yayin wannan bincike na cikin fahimta da basira, wanda ko shakka babu zai sami lada daga wajen Ubangiji.
Yayin da yake magana da ‘yan takaran zaben kuwa, Ayatullah Khamenei ya kiraye su da cewa: ‘Yan takaran da suke gudanar da yakin neman zabensu ta gidan radiyo da talabijin su san cewa suna da wani nauyi mai girma a wuyansu. Dole ne su yi taka tsantsan wajen ganin, abin Allah ya kiyaye, ba su fadi abubuwan da suka saba wa hakika ba, don kawai su janyo hankulan mutane zuwa gare su.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne maganganun ‘yan takaran su zamanto na gaskiya wadanda suka ginu bisa bayanai na gaskiya da suke da su.
Jagoran ya kara da cewa: Wajibi ne ‘yan takaran shugabancin kasa su gaya wa mutane gaskiya, wato hakikanin gaskiyar da kasar nan take ciki da kuma hakikanin gaskiya dangane da kansu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan har aka yi aiki da gaskiya, ko shakka babu Allah Madaukakin Sarki zai taimaka.
Jagoran ya ci gaba da cewa: bai kamata ‘yan takara su dinga kokarin bata sunan junansu ba da kuma murguda hakikanin yadda kasa take ciki don dai kawai su janyo hankulan mutane zuwa gare su ba.
Yayin da kuma ya koma kan kokarin da wasu suke yi na jingina ra'ayin Jagoran gare su da nuna cewa yana tare da su don samun kuri'un jama'a, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Lalle babu gaskiya cikin hakan, don kuwa babu wanda ya san ga wa Jagoran zai kada kuri'arsa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Jagora dai, kamar sauran mutane, kuri'a guda yake da ita.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan irin farfagandar da makiya suke yadawa dangane da kuri'a da kuma mahangar Jagoran kan zaben da ake gudanarwa a Iran, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Saboda cimma manufofin da aka sansu da su ne, ya sanya makiya suke ta yada irin wannan farfagandar. To amma tsarin Musulunci ba tare da la'akari da wadannan farfagandar ba, zai ci gaba da gudanar da aikinsa bisa tafarkin da ya shata da kuma manufofin da yake son cimmawa.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan ayyukan ‘yan majalisa da kuma irin nauyin da ya hau kansu kamar yadda kuma ya bayyana cewar zama dan majalisar shawarar Musulunci wata dama ce ta yin hidima ga tsarin Musulunci wanda ya zama wajibi ne a yi kokarin amfanuwa da ita.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da Dakta Ali Larijani, shugaban majalisar shawarar Musuluncin ta Iran ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyukan da majalisar ta yi tsawon shekarar da ta gabata.
1235931