IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali Ya Jaddada Bukatar Bunkasa Ci Gaban Kasar Iran

19:28 - July 11, 2013
Lambar Labari: 2559953
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya jaddada wajabcin kara zage dantse wajen gudaar da ayyukan da za su taimaka ma kasar Iran wajen kaiwa ga babban ci gaba a dukkanin bangarori.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin kara zage dantse wajen gudaar da ayyukan da za su taimaka ma kasar Iran wajen kaiwa ga babban ci gaba a dukkanin bangarori na siyasa da ilimi da sauransu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada bukatar bunkasa ci gaba kasar Iran ta kowane bangare, a ganawarsa da babban kwamandan rundunar sojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Amir Ali Hajj Zade; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewar halin da aka ciki a yanzu yana da bambanci da abin da ya faru tsawon shekaru ashirin, misalin sabanin sama da kasa ne don haka akwai bukatar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran su kara matsa kaimi tare da hada kai da kwararrun matasa da kara bunkasa ci gaba kasar Iran a kowane bangare.
Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kara da cewar dole ne al'ummar Iran su kara daura damara tare da rashin jinkiri a duk wani fagen kara bunkasa ci gaban kasa, kuma da yadda Allah za a kai ga gagarumar nasara.
A nashi bangaren babban kwamandan rundunar sojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Amir Ali Hajj ya gabatar da rahotonsa kan irin gagarumin nasarorin da bangarensa ya samu tare da irin shirye-shiryen da suke gudanarwa ta fuskar tsaro da nufin tunkarar duk wata barazana kan kasar Iran.
1256241







captcha