IQNA

Musulmin Amurka Na Raba Furanni Ga Jama’a A Jahar California

20:34 - February 16, 2015
Lambar Labari: 2858523
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a jahar California ta kasar Amurka na raba furanni ga sauran mabiya wasu addinai don abokantaka ta muslunci da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Pilot cewa, daruruwan musulmi a jahar California ta kasar Amurka, na raba furanni ga sauran mabiya wasu addinai, domin tabbatar musu da cewa addinin muslunci ba addinin tashin hankali ba ne, addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna da girmama dan adam.

Wannan mataki ya zo sakamakon abin da ya faru a jahar a ranar Talata da ta gabata, inda wani mutum mai tsananin kiyayya da musulmi da kuma addinin muslunci ya bude wutar bindiga kan wasu mabiya addinin muslunci dalibai su uku, kuma ya kashe su har lahira.

Dubban daliban jami'o'i a sassa daban-daban na Amurka na nuna juyayi da bakin cikinsu kan kisan da aka yi wa dalibai musulmi a kasar, amma kuma babu wani abu da ya yi kama da daukar kwakkwaran mataki kan wanda ya aikata wanann mummuna aiki, an dai kame shi kawai ana tsare da shi.

Kasar Amurka dai na daga cikin kasashen yammacin turai da ake cin zarafin mabiya addinin muslunci a kowane lokaci, inda mutanen da suke nuna kiayya ga muslunci suke ta karuwa a kowane lokaci, da hakan ya hada har da cikin masu tafiyar da mulki a cikin wadannan kasashe.

2856147

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha