Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban ofishin bangaren kula da harkokin kasashen ketare na cibiyar yada al'adun muslunci ya bayyana cewa an tarjama sakon jagoran juyin juya halin muslunci a cikin harsuna 21 na kasashen duniya daban-daban.
Daga cikin abin da jagora ya fada a jawabin nasa, jagoran ya yi nuni da cewa a cikin shekaru ashirin da suka gabata kasashen yamma sun yi kokarin nunawa duniya musamman matasansu cewa wannan addini mai girma abin tsoro ne, kuma shi ne makiyinsu, wanda yakamata su ji tsoronsa.
A gaskiya nuna kiyayya ga addinin Musulunci da kuma nisanta mutane daga gareshi ba wani sabon abu bane a tarihin siyasar turawan yamma da Amurka.
Baya ga haka, kasashen yamma da Amurka suna da mummunan tarihi na bautar da mutane, musamman wadanda ba kiristoci ba a duk fadin duniya, sannan ga bakar mulkin mallaka da suka yiwa kasashen duniya da dama, wanda ya hada da nuna wariyar launin fata, ko kuma fifita kibilarsu kan sauran kabilu a cikin karnuka biyar zuwa shida da suka shude.
Haka na kuma jagoran ya yi kira ga matasan da su yi dubi a cikin littafan da masu binciken tarihin kasashen yamma da Amurka suka rubuta kan yakokin mazhabobin kiristoci ta da kuma zubar da jini kan kabilanci ko yankasanci wadanda suka jawo yakokin duniya na daya nan a biyu., inda miliyoyin mutanen yankin turai da Amurka suka rasa rayukansu mummunanr siyasar shuwagabannin wadannan yankunan.
A cikin sakon jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi kira da matasan kasashen yamma da Amurka da su tambayi masu bincike da masanansu kan dalilin da ya say an siyasarsu ke katangance su kan irin sauye sauyen da ke faruwa a duniyar mu ta yau, wanda ya shafi addinin Musulunci, me yasa yan siyasar wadannan kasashe suke fada da yaduwar al-adun Musulunci a cikin kasashen turai da Amurka.
Gaskiyan lamarin shi ne irin sakonnin da halayen da addinin Musulunci yake da su, wadanda suka yi karo da manufofin shuwagabannin kasashen yamma na ci gaba da dora kansu kan mutane a duk fadin duniya, na daga cikin dalilan da suka sanyasu samar da tsoron addinin Musulunci cikin matasan kasashen su.
A wani bangaren katangance matasan kasashen yamma daga abubuwan da suka shafi kamun kai da kyatanta halaye na gari, wadanda addinai suka zo da su, hakan zai kaisu ga lalacewa ne cikin dabi’u da halaye na halaka.
Banda wannan wadan nan yan siyasa suna tarbiyantar da matasa da akidun wahhabiyawa don bata fuskar Musulunci a idanon mutanen duniya.
Daga karshen jagoran ya bukaci matasan wadannan kasashe da, na daya su yi dubi da idon basiri cikin addinin Musulunci kai tsaye tare da amfani da hankalin da All..ya basu don tabbatar da abinda ya kunsa.
Wannan zai sa su nisanci mummunan akidu masu nuna Musulunci da mummuman fusaka. Sannan na biyu kuma su sani cewa wannan musuluncin shi ne ya samar da ci gaban na azo a gani a karnuka da suka gabata , a lokacinda kasashen turai da Amurka basa da wannan ci gaban da suka samu na zahirin duniya.
2896067