IQNA

23:50 - April 25, 2015
Lambar Labari: 3206879
Bangaren kasa da kasa, Sara Omar kakar shugaban kasar Amurka ta bayyana cewa ta yi wa jikan nata addu’a a Ka’abah domin Allah yasa ya karbi addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dunyal Watan cewa, yan sa’oi kafin shugaban kasar Amurka Barack Obama ya karbi shugabancin kasar Amurka ya bayyana cewa shi mabiyin addinin kirista ne, amma wannan Magana ta kakarsa ta kara sanya shakku dangane da batun addininsa.

Sara Omar yar shekaru 88 da haihuwa dai it ace mata ta uku ga mahaifin baban Obama, kuma ta je dakin ka’abah domin gudanar da ayyukan ziyara da kuma umra, inda ta sheda wa jaridar Al-watan ta kasar Saudiyya cewa ta yid an nata addu’a domin ya zama musulmi.

Barack Obama tun kafin wanann lokacin da wasu daga cikin Amurkawa suna yada jijita cewa shi musulmi ne, amma kuma yana karyatawa inda yake ta kokarin tabbatar wa mutanen kasarsa cewa shi mabiyin addinin kirista ne, amma dk da haka wasunsu bas u amince da furucin nasa ba.

Wani jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar ta Amurka tsakanin al’ummar kasar ya nuna cewa kimanin kasha 18 daga cikin wadanda aka ji ra’ayinsu sun nuna cewa suna ganin Obama musulmi ne, yayin kasha 34 daga cikinsu ke ganin cewa shi kirista ne, amma adadin wadanda ke ganin shi musulmi ne abin yin la’akari ne.

3202548

Abubuwan Da Ya Shafa: Kenya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: