IQNA

Ofisoshin Jakadancin Iran 82 Sun Isar Da Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Turai

23:50 - June 01, 2015
Lambar Labari: 3310280
Bangaren siyasa, shugaban hukumar yada al’adu ta kasa ya bayyana cewa dukaknin ofisoshin jakdancin Iran a kasashe 82 sun yi kokari wajen isar da sakon jagora zuwa ga matasan yammacin turai.


Abu Zar Ibrahimi Turkamani shugaban hukumar yada al’adu ta kasa  a zanatawarsa da kamafanin dilalncin labaran Iqna ya ce daga abin da jagora ya bayyana akwai batun cewa, daya daga cikin abinda ya bai wa sakon na jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, muhimmanci shi ne ba wai yana kiran samarin zuwa ga fahimtarsa dangane da addinin Musulunci ba ne kamar yadda ya ke cewa, ba ni yin naciya akan cewa fahimtata da Musulunci ko kuma wata fahimta ta daban ce kadai za ku karba, abinda na ke cewa shi ne kada ku  bari wannan yanayin da ya zama ruwan dare a duniyar wannan lokacin wanda ya ke kunshe da gurbatacciyar manufa ya zama ya yi lamba.

Bugu da kari, sakon na jagoran bai yi bayani akan shi kanshi musuluncin ba ta fuskar hakikaninsa, abinda ya maida hanakli akansa shi ne cewa hakki ne na dabi’a ga kowane mutum ya sami sani sanann kuma ya gudanar da bincike da nazari domin kai wa ga hakikar da ya ke nema. Domin kuwa nesam sanin gaskiya wata dabi’a ce wacce ta ke tattare da kowane mutum.

Ibrahimi Turkamani ya ce kiran da jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ke yi ga matasa da samarin nahiyar turai yana nufin cewa; Duk wata zuciya mai neman gaskiya ta hanyar komawa zuwa ga alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah  za ta fahimci hakikanin koyarwar addinin Musulunci wacce ta ke cike da sa’adar rayuwa.

A dalilin haka, matukar samari da matasan na turai za su karanta su kuma fahimci alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah, to shakka babu za su riski cewa kungoyin irin su alqaeda da Nusrah da sauransu ba su wakiltar addinin Musulunci.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa akan sakon na jagora, wani masani dan kasar Amurka Farfesa Kevin Barrett, ya fadi cewa, a cikin alfahari na ke alfaharin watsa sakon jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Sayydi Ali Khamnei zuwa ga matasan yammacin turai wanda ya  ke kunshe da yin kira zuwa gare su da kada su mika wuya ga yanayin da ake ciki na nuna kin jinin Musulunci, ya zamana suna yin tunani cikin ‘yanci.

3309973

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha