IQNA

Bakar Siyasar Amurka Da Munanan Laifukar Sahyuniyawa Shi Ne Babbar Damuwar Musulmi

20:52 - September 23, 2015
Lambar Labari: 3366899
Bangaren siyasa, Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khameni jagoran juyin juya halin muslunci ya fadi a cikin sakonsa ga mahajjatan bana cewa, babbar damuwar musulmi a halin yanzu ita ce bakar siyasar Amurka da munanan laifukan sahyuniyawa da keta alfarmar masallacin Aqsa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagoran juyin Islama cewa, a cikin da ya aike zuwa ga mahajjatan bana, Ayatollah Sayyid Ali Khamne jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana damuwar musulmi a halin yanzu da cewa ita ce bakar siyasar Amurka da munanan laifukan sahyuniyawa da suke aikatawa da kuma keta alfarmar masallacin Aqsa masallaci mai tsarki, ya ce ya zama wajibi kan malamai da masana su yi amfani da wannan dama ta hajji wajen bayyana matsayi na barranta.

Dangane da rasuwar mahajjata kuwa, ya bayyana abin da ya faru da cewa abin alhini ne, tare da yin adduar Allah ya ji kansu da rahama baki daya.

A yau ne a safiyar Laraba wakilin Waliyul Faqih Hojjatol-eslam Kadhi Askar kuma jagoran alhazan Iran ya karanta sakon na jagora a filin Arafah, kamar haka:



Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai



Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban halittu gaba daya Muhammad da Alayensa tsarkaka da kuma zababbun sahabbansa da mabiyansu cikin kyautatawa har zuwa tashin alkiyama.



Sallama da aminci su tabbata ga (Dakin) Ka’aba mai girma, cibiyar tauhidi, wajen dawafin muminai kana wajen saukar Mala’iku. Haka nan aminci ya tabbata ga Masjid al-Haram da Arafa da Mash’ar da Mina. Aminci ya tabbata ga zukata masu tsoron Allah da harsuna masu ambaton Allah, da idanuwan da suke bude cikin basira da tunani da suka kama hanya ta daukar darasi; sannan kuma aminci ya tabbata a gare ku, Ya ku Mahajjata, wadanda kuka sami nasarar amsa kiran Ubangiji sannan kuma kuka zauna kan wannan tabarma (akwashi) mai cike da ni’ima.



Nauyi na farko (da ke wuyanmu) shi ne tunani cikin wannan amsa kira na duniya kuma na har abada, na cewa: Hakika godiya da ni’ima da mulki na ka ne. Babu abokin tarayya a gare ka, lalle mun amsa maka. Wato dukkanin yabo da godiya naka ne, haka nan dukkanin ni’imomi daga gare ka suke, haka nan dukkanin mulki da karfi naka ne. Wannan shi ne kallo na farko da fatan da ake da shi daga wajen mahajjaci a yayin wannan farali da ke cike da ma’ana, sannan kuma a ci gaba da sauran ayyukan hajjin za a samu alaka da tafiya tare tsakanin wadannan abubuwa tamkar dawwamammiyar koyarwa da kuma wani darasi da ba za a taba mantawa da shi ba da za a gabatar masa, sannan kuma a bukace shi da ya tsara rayuwarsa karkashin wannan tushe. Koyon wannan darasi mai girma da kuma aiki da shi, zai zamanto mabubbuga mai cike da albarkoki wacce za ta iya sabunta rayuwar musulmi da kyautata ta, kana da kuma fitar da su daga cikin tsaka mai wuyan da suke ciki – a wannan zamani da kuma dukkanin zamunna -. Lalle ana iya ruguza gumakan son rai da girman kai da sha’awa, gumakan neman mulki da amincewa da ikon wasu, gumakan ma’abota girman kan duniya, gumakan kasala da rashin jin nauyi a wuya, kai da ma dukkanin gumaka masu wulakantar da matsayin dan’adam, ta hanyar riko da wannan kira na (Annabi) Ibrahim, idan har hakan ya sami wajen zama a cikin zukata sannan kuma ya zamanto tsarin rayuwa. Sannan kuma ‘yanci da daukaka da zaman lafiya za su maye gurbin dogaro da wasu da wahalhalu da bala’oi.



‘Yan’uwa maza da mata Mahajjata, daga kowace al’umma ko kasa kuka fito, ku yi tuntuni cikin wannan kalma mai cike da hikima ta Ubangiji, sannan kuma ta hanyar dubi da idon basira cikin irin matsalolin da duniyar musulmi take ciki musamman a Yammacin Asiya da Arewacin Afirka, ku yi iyakacin kokarinku gwargwadon irin karfi da dama ta mutum da kuma inda yake raye wajen sauke nauyin da ke wuyanku dangane da wadannan matsalolin.



A halin yanzu siyasar ashararanci ta Amurka a wannan yanki ta kasance ummul aba’isin din haifar da yaki da zubar da jini da ruguza kasa da sanya wasu zama ‘yan gudun hijira, haka nan kuma ta haifar da talauci da ci baya da sabani na kabilanci da mazhaba. A bangare guda kuma zaluncin haramtacciyar gwamnatin Sahyoniyawa a kasar Palastinu ya kai matsayin koli na muni. Ana ci gaba da keta hurumin Masallacin Al-Aqsa mai alfarma da kuma ci gaba da zubar da jini da sace dukiyar Palastinawa da ake zalunta. Hakan ya zamanto babbar matsalar da ke gabanku, Ya ku musulmi, wadda wajibi ne ku yi tunani kanta da kuma ganin kun samo hanyar da za ku sauke wannan nauyi na Musulunci da ke wuyanku.



Malaman addini da manyan ‘yan siyasa da sauran masana suna da gagarumin nauyi a wuyansu. Sai dai abin bakin cikin shi ne cewa a mafi yawan lokuta an mance da wannan nauyin. Maimakon malamai su ba da himma wajen kunna wutar sabani na mazhaba, haka nan su ma ‘yan siyasa maimakon nuna gazawa wajen tinkarar makiya, haka nan su ma masana maimakon su shagaltu da lamurra na bayan fage, kamata yayi su fahimci matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta sannan su sauke nauyin da ke wuyansu a gaban Allah. Lamurra masu tada hankali da suke faruwa a yankin nan, a Iraki da Siriya da Yemen da Bahrain, da Yammacin (Kogin Jordan) da Gaza, haka nan a wasu kasashen Asiya da Afirka, sun kasance babbar matsalar al’ummar Musulmi wanda ko shakka babu akwai hannun ma’abota girman kan duniya cikin hakan, sannan kuma a yi tunanin yadda za a magance wadannan matsalolin. Wajibi ne al’ummomi su bukaci (magance) wannan matsalar daga wajen gwamnatocinsu, su kuwa gwamnatocin wajibi ne su sauke wannan gagarumin nauyi da ke wuyansu.



Aikin hajji da wannan gagarumin taro na jama’a kuwa, shi ne wajen da ya fi dacewa wajen bayyana da kuma kokarin sauke wannan nauyin.



(Taron) Barranta (daga mushirikai), wanda wajibi ne dukkanin alhazai daga duk inda suke su shigo cikinsa, daya daga cikin fitattun ayyuka na siyasa na wannan farali na hajji.



A wannan shekarar hatsari mai bakanta rai da ya faru a Masjid al-Haram wani lamari ne da ya bakanta ran alhazai da al’ummominsu. Na’am, wadanda wannan hatsari ya ritsa da su sun koma ga Ubangijinsu ne alhali suna cikin salla da dawafi da ibada, sun sami babban rabo muna fatan Allah Ya tashe su cikin rahama da kulawarsa, insha Allah. Lalle hakan babban tausar zuciya ce ga iyalansu. To amma hakan ba zai iya rage irin nauyin da ke wuyan wadanda nauyi kula da lafiya Bakin Allah yake wuyansu ba. Don haka muna kiran da su dau wannan nauyin da kuma sauke shi.



Amincin Allah Ya tabbata ga bayinsa sahilai.



Sayyid Ali Khamenei



4, Zul Hajj 1436 (Hijira Qamariyya)



27, Shahrivar, 1394 (Hijira Shamsiyya)



18, Satumba, 2015 (Miladiyya)



3366588

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha