IQNA

Alhakin Wannan Babbar Faji’a Yana Kan Saudiyyah / Dole Ne Ta Nemi Uzuri Daga Al’ummar Musulmi

23:50 - September 27, 2015
Lambar Labari: 3372480
Bangaren siyasa; Jagoran juyin juya halin Musulunci a lokacin da yake gabatar da darasinsa na "Bahasul Kharij" yayi karin haske dangane da turmutsitsin da ya faru a Mina da yayi sanadiyyar mutuwa da raunata wani adadi mai yawan gaske na mahajjatan da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Al'ummar musulmi suna da tambayoyi masu yawa dangane da wannan lamarin. Don haka mahukuntan Saudiyya, maimakon dora alhakin hakan kan wasu, wajibi ne su nemi afuwar al'ummar musulmi da iyalan da suke cikin makoki sannan kuma su sauke wannan gagarumin nauyi da ke wuyansu.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da wannan lamari mai sosa rai da ya faru a Mina da kuma yadda ya mayar da ranar idin al'ummar musulmi zuwa ga zaman makoki, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Babu yadda za a yi mutum ya cire kansa daga tunanin wannan abin bakin ciki mai sosa rai ko na dan karamin lokaci ne kuwa. Hakika cikin kwanakin nan wannan lamari yayi girma da nauyi a zukatanmu da na dukkanin musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin kokarin da mahukuntan Saudiyya suke yi na kin daukar alhakin abin da ya faru da kuma kokarin dora alhakin hakan a kan wasu na daban a matsayin wani lamarin da bai dace ba wanda kuma babu wani tasiri da zai yi inda ya ce: Al'ummar musulmi suna da tambayoyi da yawa don kuwa mutuwar sama da mutane dubu ba karamin abu ba ne. A saboda haka wajibi ne duniyar musulmi su fara tunanin hanyar magance wannan matsalar.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Ba za a taba mancewa da wannan lamari ba. Sannan kuma al'ummomi za su ci gaba da sanya ido da kuma dubi cikin wannan lamarin da dukkan karfinsu. A saboda haka wajibi ne jami'an Saudiyya su amince da laifinsu kana kuma su nemi afuwa da gafarar al'ummar musulmi da iyalan wadanda abin ya ritsa da su, maimakon tuhumar wannan da wancan.

3370995

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha