IQNA

Hamas Ta Kira Da A Ci Gaba Da Intifada / Harin Kunar Bakin waken yara Biyu A Baitul Muqaddas

22:35 - November 10, 2015
Lambar Labari: 3446873
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hamas ta bayyana cewa ci gaba da kame manyan jagororinta ba zai taba hana kungiyar ci gaba da ayyukanta ba da kuma gwagwarmaya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahabarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine cewa, a yau kungiyar Hamas ta bayyana cewa ci gaba da kame manyan jagororinta ba zai taba hana kungiyar ci gaba da ayyukanta ba da kuma gwagwarmaya domin yancin palastinu.

Wannan kira ya zo bayan matakan haramtacciyar kasar Israi;a ta dauka na kame anyan jagororin wanann kungiya  acikin kwanakin nan da nufin kara raunana kungiyar.

A cikin makon nan an kame manyan jagoron wannan kungiya a yankin Kalkiliyyah da ke cikin yankunan gabar yamma da kogin jodan, wanda hakan ke nufin cewa Sahyuniyawa ba za su daddara ba.

Wasu Matasa Palastinawa 2 Sun Yi Shahada A Gabacin baitul Maqdis

Wani matashi bapalastine ya yi shahada a yau bayan da jami’an tsaron yahudawan sahyuniya suka bude wutar bindiga a kansa a yankin Babul Amud da ke cikin birnin Quds.

Majiyar ‘yan sanadan Isra’ila ta ce jami’an tsron yahudawa sun harbe matashin ne tare da wani abokinsa wadanda shekarunsu bas u 12 zuwa 13 ba, bisa zarginsu da kokarin daba wa wani bayahude wuka, a nan take daya daga cikin matasan ya yi shahada, dayan kuma ya samu munanan raunuka, wanda yanzu ake kokarin ceto rayuwarsa a wani asibiti da ke birnin Quds.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama  aduniya suna zargin Isra’ila da yin hawan kawara kan dokokin kasa da kasa wajen cin zarafin Palastinawa, ta hanyar yi musu kisan gilla da rushe musu gidaje da kuma wurarensu na ibada da suka hada da masallatai da majami’u, wanda hakan kan sanya Palastinawan daukar matakan kare kansu daga wannan zalunci.

3446726

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha