IQNA

Bayar Da Dama Ga Mutane Kan Lamarin Muslunci Zai Karfafa Hanyoyin Dakile Tunani Na Ta’addanci

23:33 - November 22, 2015
Lambar Labari: 3455816
Bangaren siyasa, Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Turkmenetan ya bayyana cewa, hanyar yaki da ta’addanci da dakile shi ita ce karfafa mutane kan lamarin addini bisa sahihiyar hanya.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a yammacin yau Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Turkeministan Gurbanguly Berdimuhamedow da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma.

Yayin da yake ishara da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Turkeministan da kuma irin damar da ake da ita na kara fadada wannan alakar da kuma batun fada da ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin nan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Hanyar fada da wadannan kungiyoyi na ‘yan ta'adda da kuma kawo karshen irin tasirin da suke da shi, ita ce bayyanar da koyarwar Musulunci na hakika wadanda suka yi daidai da hankali.

Ayatullah Khamenei ya bayyana al'ummomin kasashen Iran da Turkeministan a matsayin al'ummomi biyu makwabtan juna. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin damar da ake da ita wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Jagoran cewa yayi: Wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar jin dadin da ci gaban kasashen makwabta da sauran kasashen musulmi lamari ne da Iran take fatan gani wanda kuma zai amfani Jamhuriyar Musulunci ta Iran, daga nan sai ya ce: Iyakokin kasashen Iran da Turkeministan iyakoki ne na sulhu da kwanciyar hankalin dukkanin kasashen biyu.

Yayin da yake ishara da batun tsaron kasashen Iran da Turkeministan a irin yanayin rashin tsaron da ake fuskanta a halin yanzu a yankin Gabas ta tsakiya, Jagoran ya bayyana karfafa irin alakar da ke tsakanin biyu a matsayin wani lamari da ya zama wajibi inda ya ce: Don fada da kawo karshen ayyukan ta'addancin rashin imani na kungiyar Da'esh (ISIS) da sauran kungiyoyi masu kafirta musulmi irin ta wadanda suke aikata danyen aikinsu da sunan Musulunci, wajibi ne a share wa mutane fagen aiwatar da koyarwar Musulunci ta hakika. Hanyar da ta fi dacewa wajen kawo karshen irin tasirin da wadannan kungiyoyi suke da shi, ita ce karfafa ayyuka na tunani da al'adu na Musulunci da suka yi daidai da hankali.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin ayyukan rashin imani da kungiyoyin ‘yan ta'addan suke aikatawa d a suka hada da yankan rago da suke wa mutane da kuma kona su da wuta a matsayin wani abin da ke tabbatar da cewa wadannan mutane sun yi hannun riga da addinin Musulunci. Don haka sai ya ce: Musulunci dai addini ne na ‘yan'uwanta, kauna da fatan alheri da sauran al'ummomi. Ko shakka babu irin wadannan ayyukan ta'adanci da suke yi, ba shi da wata alaka da addinin Musulunci.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Turkeministan Gurbanguly Berdimuhamedow wanda mataimakin shugaban kasar Iran Malam Eshaq Jahangiri yake wa jagoranci ya bayyana farin cikinsa da ziyarar da ya kawo Iran yana mai cewa ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci wata dama ce kana kuma abin alfahari a gare shi inda ya ce: A koda yaushe Iran da Turkeministan sun kasance masu kyakkyawar alaka a tsakaninsu. Maganar da ka yi na cewa Iran da Turkeministan ba wai kawai makwabta ba ne face dai ‘yan'uwan juna ne wani lamari ne da faranta rai da karfafa gwiwan gwamnati da al'ummar Turkeministan.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan nasihohin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi masa a ziyarar da ya kawo masa a baya, shugaban kasar Turkeministan ya bayyana cewar: Maganganunka a matsayin wani Jagora kana kuma masani wani lamari ne da ke da kimar gaske a gare mu, sannan kuma irin wadannan nasihohi sun kasance masu amfani sosai a gare mu.

Har ila yau kuma yayin da yake da magana kan irin damar da ake da ita wajen fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu musamman a bangaren iskar gas, sufuri da kuma gina hanyoyi, shugaba Gurbanguly Berdimuhamedow ya bayyana cewar: Ayyukan ci gaban kasa da karfafa tattalin arziki tsakanin Iran da Turkeministan wani lamari ne da zai amfani dukkanin kasashen yankin nan.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan mummunan yanayi na rashin tsaro da yankin nan ke fuskanta, shugaban na Turkeministan yayi ishara da ayyukan ta'addancin kungiyar Da'esh inda ya ce: Kungiyar Da'esh da makamantanta ko kamshin Musulunci ba su shaka ba. Amma abin bakin cikin shi ne cewa wasu gwamnatoci ne suke goyon baya da daure mata gindi.

3455793

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha