IQNA

An Tarjama Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Turaia Cikin Harsuna 23

15:31 - November 30, 2015
Lambar Labari: 3458724
Bangaren kasa da kasa, an tarjama wasikar jagora ta biyu zuwa ga matasan nahiyar turai a cikin harsuna 23.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hajj.ir cewa, a cikin sakon nasa jagoran juyin juya halin Musulunci ya ja hankalin matasan nahiyar turai da su zama cikin fadaka dangane da irin farfagandar da ake yadawa dangane da addinin muslunci a cikin kasashensu, tun bayan kai harin Faransa musamamn ma yadda ake kokarin danganta addanin muslunci da ayyukan ta’addanci, alhali ta’addancin da ake gani sakamako ne na siyasar kasashen yammacin turai da kawayensu na yankin gabas ta tsakiya.

Jagoran ya yi ishara da irin matsanancin halin da aka jefa  ala’ummar palastinu tsawon shekaru fiye da sittin da suka gabata, inda yahudawan sahyuniya tare da goyon bayan Amurka da sauran kasashen turai suke yin kisan gilla a kan Palastinawa, wanda hakan babban ta’addanci ne da duniya ta kawar da kai a kansa.

Daga karshe ya kiraye matasan na turai da su bincike addinin muslunci da koyarwarsa, kuma su san addinin muslunci ta hanyar da ta dace, idan suka yi haka za su gane cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da kare hakkin dan adam, sabanin abin da ake sanar da su.

An tarjama wannan sako a cikin harsuna kimanin 23 na duniya daga ciki har da larabci, turanci, jamusanci, Urdu, Spananci, Faransanci, Turkanci, Azari, Hindi, Bosnia, Albani, Rusi, Uzbaki, Dari, Itali, Hausa, Swahili, Chini, Armani, Japani, Bangala da kuma Tukaman.

3458625

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha