Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na
ofishin jagora tarjamar matanin bayanin nasa da ke cewa, a jawabin da ya
gabatar yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya
taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah
(s.a.w.a) da Imam Sadiq (a.s) inda ya bayyana kokari ba kama hannun yaro
wajen sake rayar da ruhi na hakika na addinin Muuslunci a wannan duniya
wacce take cike da zalunci da nuna wariya da rashin imani a matsayin
daya daga cikin mafi muhimmancin nauyin da ke wuyan duniyar musulmi a
halin yanzu musamman a tsakanin malamai da masana. Jagoran ya ci gaba da
cewa: A halin yanzu dai lokaci ne da duniyar musulmi da za ta mike
wajen tabbatar da ci gaba iri na Musulunci ta hanyar amfani da ilimi,
hanyoyi na zamani da kuma hankali, hikima da basira.
Ayatullah
Khamenei ya bayyana gudanar da bukukuwan maulidin Annabi (s.a.w.a) kawai
a matsayin wani karamin aiki idan aka kwatanta irin gagarumin nauyi da
fatan da ake da shi a kan duniyar musulmi inda ya ce: A halin yanzu
nauyin da ke wuyan al'ummar musulmi bai takaita kawai ga gudanar da
bukukuwan maulidi ko ranar aiko Ma'aiki (s.a.w.a) ba, face dai wajibi ne
duniyar musulmi ta ba da himma da muhimmanci wajen isa ga hakikanin ci
gaba da kuma koyarwa ta Musulunci.
Jagoran ya ci gaba da cewa:
Sabuwar wayewa ta Musulunci ba tana nufin wuce gona da iri kan kasashe,
take hakkokin bil'adama da kuma tilasta wa al'ummomin halaye da
al'adunsu tamkar irin abin da al'adu da ci gaban yammaci ya aikata. Face
dai abin nufi shi ne gabatar da kamala da nagarta ta Ubangiji ga
bil'adama da kuma share fagen da mutum zai gano wa kansa ingantacciyar
hanya da kuma tafarki.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin
yadda kasashen yammaci suka yi amfani da ilimi da falsafar duniyar
musulmi wajen kafa irin ci gabansu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin
ya bayyana cewar: Irin wannan ci gaban, duk kuwa da a zahiri ya gabatar
da abubuwa masu kyau da suka hada da fasaha, sauki da kayayyakin aiki na
saukake rayuwa, to amma dai bai samar wa dan'adam da farin ciki da
sa'ada da kuma adalci ba. Sannan ana samun karo da junan a cikinsa.
Ayatullah
Khamenei ya kara da cewa: Ci gaban yammaci duk da irin kyawu na zahiri
da yake da shi, amma a halin yanzu a bangaren kyawawan halaye da ababe
masu kusata mutum da Allah ya zamanto holoko, ta yadda hatta su kansu
mutanen yammaci suna fadin hakan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara
da cewa a halin yanzu dai lokaci ne na duniyar musulmi su gabatar da
kuma kafa tushen koyawa da al'adun Musulunci da gabatar da shi ga
duniya, Jagoran cewa yayi: Don isa ga wannan manufar, lalle babu wani
fata da ake da shi a kan ‘yan siyasar duniyar musulmi. Don haka wajibi
ne malami da masanan da ba su dauki kasashen yammaci a matsayin
alkiblarsu ba, su mike wajen wayar da kan musulmi da kuma fahimtar cewa
lalle ana iya kafa tushen wannan ci gaban.
Haka nan kuma yayin da
yake ishara da irin dama da karfin da duniyar musulmi take da shi da
suka hada da kasa mai kyau, bigire mai kyau wanda kuma ya dace,
albarkatun kasa ba iyaka da kuma al'ummar da suke cikin shiri, Jagoran
juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Matukar aka hada irin wannan
karfi da dama da ake da su da hakikanin koyarwar Musulunci, to kuwa
al'ummar musulmi za ta iya bayyanar da irin wannan kwarewa da take da
shi a fagagen ilimi da siyasa da fasaha da kuma zamantakewa.
Ayatullah
Khamenei ya bayyana tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin
misalin da ke tabbatar da yiyuwar isa ga wannan manufa mai girma, daga
nan sai ya ce: Iran, kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, ta ci
baya ainun a fagen ilimi, siyasa da zamantakewa. A fagen siyasa ta
kasance saniyar ware, a fagen gudanar da kasa kuwa ta kasance ‘yar
amshin shata. Amma a halin yanzu albarkacin Musulunci, al'ummar Iran ta
bayyanar da irin matsayi da mutumcin. Ta zamanto kasa ma'abociyar ci
gaba mai muhimmanci a fagen ilimi da fasaha da ilmummuka na zamani. Ta
zamanto daga cikin kasashen da suke a sahun gaba-gaba a wadannan fagage.
Jagoran
ya bayyana cewa ana iya tabbatar da wannan misali a dukkanin kasashen
musulmi. Jagoran ya ce: Akwai sharadin isa ga wannan matsayin, sharadin
kuwa shi ne raje irin ikon da ‘yan mulkin mallaka na duniya suke da shi a
kan al'ummomi, duk kuwa da cewa akwai wahalhalun da za a fuskanta. Don
kuwa ba za a iya cimma wata babbar manufa ba tare da wahala ba.
Yayin
da yake jaddada cewar a mahanga da ci gaban Musulunci, sabanin ci gaban
yammaci, ba a tilasta wa wata kasa da karfin tuwo ta shigo ciki,
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Yayin kafa sabuwar
ci gaban musulmi, bai kamata mahangarmu ta koma ga kasashen Yammaci ba.
Bai kamata mu damu da fara'a da sakin fuskarsu ba. Face dai wajibi ne mu
ci gaba da tafiya a bisa ingantaccen tafarki ta hanyar dogaro da irin
karfin da muke da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar daya daga
cikin hanyoyin da makiya suke bi wajen ganin sun hana kafuwar wannan ci
gaba na Musulunci shi ne haifar da rarrabuwan kai tsakanin al'ummar
musulmi, daga nan sai ya ce: Daga lokacin da jami'an Amurka suka fara
maganar kan Shi'a da Sunna, tun daga lokacin masana da masu fahimta suka
fara nuna damuwa, don kuwa a fili yake cewa suna shirin kulla wani
sabon makircin ne wanda ya fi wadanda suka kulla a baya hatsari.
Haka
nan yayin da yake jaddada cewa Amurkawa suna adawa ne da asalin
Musulunci, da kuma cewa bai kamata a fada tarkonsu kan maganganun da
suke yi na nuna goyon bayan wani bangare ba, Jagoran cewa yayi:
Maganganun da tsohon shugaban kasar Amurka yayi bayan harin 11 ga watan
Satumba na batun yakin salibu (crusade), a hakikanin gaskiya hakan wata
alama ce ta yakin ma'abota girman kai da Musulunci.
Har ila yau kuma
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana maganganun jami'an Amurka
na yanzu kan goyon bayan Musulunci a matsayin wani abu da ya saba wa
hakikanin abin da ke gudana a kas sannan kuma wata alama ce ta
munafuncinsu. Jagoran ya ci gaba da cewa: Jami'an Amurka na yanzu ma
suna adawa da asalin Musulunci. Sannan kuma sabanin abubuwan da suke
fadi, suna kokarin haifar da rarrabuwan kai ne tsakanin musulmi. Misalin
hakan kuwa shi ne samar da kungiyoyin ta'addanci irin su Da'esh da
sauran kungiyoyi na daban da aka samar da su daga kudaden ‘yan amshin
shatan Amurkan da goyon bayansu nasiaysa, sannan kuma suna ta aikata
danyen aikin dake faruwa a duniyar musulmi.
Ayatullah Khamenei ya
bayyana maganganun da jami'an Amurka suke yi na nuna goyon bayansu ga
‘yan Sunna da kuma adawa da ‘yan Shi'a a matsayin karya tsagoronta inda
ya ce: Shin al'ummar Gaza wadanda suke fuskantar irin wannan bakin
zalunci da kisan kiyashin ba ‘yan Sunna ba ne ko kuma mutanen Yammacin
Kogin Jordan da su ma suke fuskantar irin wannan mafi munin matsin
lambar, ba ‘yan Sunna ba ne?
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da
maganar wani jami'in Amurka na cewa ‘Riko da Musulunci shi ne makiyin
Amurka', Jagoran ya ce: A wajen Amurkawa babu wani bambanci tsakanin
Shi'a da Sunna. Suna adawa ne da duk wani mutumin da yake son rayuwa
karkashin hukunce-hukunce da kuma dokoki na Musulunci sannan kuma yake
kokari wajen cimma hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya
bayyana cewar babbar matsalar Amurkawa da musulmi ita ce riko da koyarwa
da kuma hukunce-hukuncen Musulunci da kuma kokari wajen kafa tushen ci
gaban Musulunci. Daga nan sai ya ce: Bisa wannan dalilin ne ya sanya
daga lokacin da farkawar Musulunci da aka samu ta kunno kai, suka shiga
cikin damuwa da kuma kokari wajen ganin sun kawar da ita, wanda sun sami
nasarar hakan a wasu kasashen. To amma dai farkawar Musulunci ba abu ne
da za a kawar dashi ba. Kuma cikin yardar Allah za ta kai ga manufarta.
Ayatullah
Khamenei ya bayyana cewa babbar manufar ma'abota girman kai ita ce
haifar da yakin basasa tsakanin musulmi da kuma ruguza tushen kasashen
musulmi irin su Siriya, Yemen da Libiya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Bai
kamata a zuba ido dangane da wannan makircin ba, face dai wajibi ne a
yi tsayin daka wajen tinkarar wannan makirci ta hanyar amfani da basira
da tsayin daka.
Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga shirun
da duniyar musulmi suka yi dangane da ci gaba da matsin lambar da ake yi
wa musulmin kasar Bahrain haka nan da kuma ci gaba da ruwan bama-baman
da ake yi ba dare ba rana a kasar Yemen, da kuma yanayin da kasashen
Siriya da Iraki suke ciki da kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan
a Nijeriya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Me ya
sa duniyar musulmi ta yi gum da bakinta dangane da irin wannan bala'i
mai sosa rai da aka yi wa wannan malami mai son kawo gyara, hadin kan
(musulmi) kuma mumini, kana aka kashe kimanin mutane dubu da kuma kashe
masa ‘ya'yansa?
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa:
Manufar makiyan Musulunci tana da hatsarin gaske. Nauyin da ke wuyan
kowa shi ne amfani da basira da kuma farkawa. Sannan kuma a irin wannan
yanayin nauyin da ke ruwan malaman Musulunci da masana na gari shi ne su
yi magana da mutane da kuma ‘yan siyasar da suke da lamiri da kuma
bayyanar musu da hakikanin lamarin.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da
cewa: A yayin da masu tinkaho da karfi na duniya suke kokarin aiwatar da
bakar aniyarsu a kan duniyar musulmi da dukkan karfinsu, lalle bai
kamata wani ya gafala da rufe ido kan hakikanin abin da ke a kas ba.
Kafin
jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban kasar Iran
Sheikh Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa, inda yayin da yake taya
al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Ma'aikin Allah
(s.a.w.a) da Imam Sadiq (a.s), shugaba Ruhani ya bayyana Manzon Allah
(s.a.w.a) a matsayin babban abin koyi a fagen kyawawan halaye da tsarki.
Shugaba Ruhani ya ci gaba da cewa: Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya zo wa
duniya da darasin hadin kai da ‘yan'uwantaka.
Haka nan kuma yayin da
yake bayanin cewa a halin yanzu aka bukatar riko da koyarwar Annabin
Rahama (s.a.w.a) sama da lokutan da suka gabata, shugaban na Iran ya
bayyana cewar: Albarkacin hadin kan al'umma da kuma shiryarwar jagoranmu
mai girma sun sami damar samun nasara a kan ma'abota tinkaho da karfi
na duniya, kuma wannan nasarar za ta ci gaba da wanzuwa.
Haka nan
kuma yayin da yake ishara da zabubbuka guda biyu da suke gaban al'ummar
Iran, wato zaben ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci da kuma ‘yan
majalisar shawarar Musulunci, shugaba Ruhani ya bayyana wadannan
zabubbuka guda biyu a matsayin babbar jarabawa ga al'ummar Iran don haka
sai ya ce: Wajibi ne kowa ya zamanto yana tunanin nasarar tsarin
Musulunci da kuma kasar Iran ne a yayin wannan zaben.
Har ila yau
shugaba Ruhani yayi ishara da gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi
a ranar 9 ga watan Dey 1388 (1999 bayan rikicin zaben shugaban kasa da
aka gudanar) don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na Iran inda ya
ce: Ranar 9 ga watan Dey, rana ce da al'ummar Iran suka fito don kare
Gidan Annabci, don kare tsarin Musulunci, dokar kasar da kuma tsarin
Wilayatul Fakih da kuma Waliyul Fakih din.
Shugaba na Iran ya ci gaba
da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami irin tsaro da kwanciyar
hankalin da take ciki ne albarkacin tsare-tsare da kuma hikima da hangen
nesan Jagoran juyin juya halin Musulunci. Don haka za mu iya gode wa
wannan ni'imar ce ta hanyar kara hadin kai da kuma taimakon duniyar
musulmi wajen ‘yantar da kasashen (duniya) daga ta'addanci da kuma tsoma
bakin ‘yan kasashen waje.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa
makiya sun sanya kasashen musulmi fada da junansu, shugaba Ruhani ya
bayyana cewar: Matukar manyan kasashen musulmi suka hada kansu suna masu
tunanin matsalolin da suke fuskantar musulmi gaba daya, to kuwa cikin
sauki za su iya magance matsalolin da suke fuskantarsu.
Har ila yau
yayin da yake bayanain cewa wasu kasashen musulmin maimako a ce sun yi
kokarin hada kai da kulla mu'amala ta al'adu da tattalin arziki da
junansu amma sai suka koma wajen wasu kasashe da suke wajen wannan
yankin nan, Shugaban na Iran ya bayyana cewar: Abin bakin ciki ne yadda
wata kasa take bakin cikin nasarar da wata al'umma ta samu a fagen
siyasa da kuma mika irin karfi na siyasa da duniyar musulmi take da shi
zuwa ga manyan kasashen duniya ‘yan waje.
Shugaban na Iran ya ci gaba
da cewa: Kasar da ta taka gagarumar rawa wajen faduwar farashin man
fetur, amma a yanzu sai ga shi tana fuskantar matsalar tattalin arziki
cikin kasafin kudinta na shekara, wanda lamari ne ke nuni da cewa in za
ka gina ramin mugunta gina shi gajere.
Daga karshe dai Jagoran juyin
juya halin Musulunci ya gaisa hannu da hannu da wani adadi mai yawa na
baki ‘yan kasashen waje da suka halarci taron Makon Hadin Kai.
3470656