IQNA

Sakon Jagora Na Rasuwar Ayatollah Wa’iz Tabasi:

Shi Ya Kasance Dan UwaAboki Gare Ni Kuma Mai Bin tafarkin Imam

23:46 - March 06, 2016
Lambar Labari: 3480206
Bangaren siyasa, bayan rasuwar Ayatollah Sheikh Abbas waiz tabasi, jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya isr da sakon ta’aziyya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, bayan sanar da rasuwar babban malami, mujahidi sannan kuma daya daga cikin manyan magoya bayan juyin juya halin Musulunci Ayatullah Hajj Sheikh Abbas Wa'iz Tabasi, yardar Allah ta tabbata a gare shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da wani sako na ta'aziyya saboda wannan babban rashi da aka yi.

Abin da ke biye fassarar sakon Jagoran juyin juya halin Musuluncin ne:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Cikin tsananin bakin ciki da alhini na samu labarin rasuwar babban malami, mujahidi sannan kuma abokin juyin juya halin Musulunci na gaskiya mai girma Hujjatul Islam wal muslimin Hajj Sheikh Abbas Wa'iz Tabasi, yardar Allah ta tabbata a gare shi. Lalle ya kasance dan'uwa, masoyi sannan kuma aboki na kurkusa a gare ni, kamar yadda kuma ya kasance masoyi sannan kuma mabiyin marigayi Imam (Khumaini) kana kuma tsayayyen mai hidima da riko da juyin juya halin Musulunci da dukkan karfinsa. Tun farko-farkon gwagwarmayar yunkurin Musulunci, birnin Mashhad ya shaidi kasantuwar wannan malami mai girma da kuma tasirinsa a fagage masu cike da hatsari da wahalhalu. Sannan kuma ya ci gaba da kasantuwa a wannan fagen har zuwa ranakun karshe na wannan gwagwarmaya ta al'ummar Iran.

Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, irin yarda da shi da marigayi Imam yayi ne ya ba shi damar samun wannan abin alfahari na kula da hubbaren Imam Ridha, amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda ya gudanar da hidima maras tamka a wannan hubbaren cikin himma da azama. Muna rokon Allah da ya sanya shi karkashin kulawar wannan mai girma. Batun riko da juyin juya halin Musulunci da kuma mika kai ga koyarwa da manufofin tsarin Musulunci da kuma kokari a wannan tafarkin mai wahalar gaske wanda a mafi yawan lokuta ba ma da bayyanar da shi a fili ba, shi kansa hakan wani fasali ne na rayuwar wannan malami mai girman matsayi. A halin yanzu dai bayan rasuwarsa, a hakikanin gaskiya na rasa dan'uwa mai tausayi sannan kuma abokin zama a lokacin bakunta da tsanani kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, kana kuma abokin aiki ba kama hannun yaro bayan nasarar juyin juya halin Musulunci. A saboda haka ina rokon Allah Mai Rahama da Ya ba shi ladar da ta dace da kuma gafara da yarda ta Ubangiji a gare shi.

Ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalansa masu girma da kuma abin da ya bari musamman matarsa ma'abociya hakuri da kyautatawa da kuma ‘ya'yansa masu girma. Ina rokon Allah da ya ba su hakuri da dauriyar jurewa wannan rashi da aka yi.

Sayyid Ali Khamenei

14, ga watan Esfand, 1394

(04, Maris, 2016)

3480452

captcha