IQNA

Kyautata Ayyukan Cibiyoyin Kur’ani Fiye Da Dubu 17 A Senegal

23:06 - May 02, 2016
Lambar Labari: 3480371
Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar hadin kan makarantun kasar Senegal ya gana da shugaban ofishin yada al’adu na kasar Iran a Senegal inda ya sheda masa cewa sun gana da shugbannin makarantu dubu 17.
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dakar.icro cewa, Sayyid Hassan Esmati shugaban ofishin yada al’adu na kasar Iran a Senegal ya gana da shugaban kungiyar hadin kan makarantun Senegal Sheikh Musatafa Lu a yankin Chare da ke cikin birnin Dakar fadar mulkin kasar.

Shugaban ofishin yada al’adun na Iran ya bayyana cewa kasarsa tana bayar muhimmanci matuka ga sha’anin kur’ani musamman jagoran juyin juya hali Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei wanda shi ne ya kirkiro wani shi, wanda ke fatan ganin an samu mahardata kur’ani miliyan 10 a Iran.

Bangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da ska shafi kara karfafa ayyukan da suka shafi makarantun kur’ani a kasar, musamman ganin cewa kasar Senegal tana daga cikin kasashen da suke bayar da muhimmanci a wannan bangare.

Wannan shiri dai da kungiyar take da shin a nufin ganin an samar da wani tsari ga dukkanin makarntu na kur’ani, musamman ma ganin cewa wasu da dama daga cikinsu bas u da rijista, saboda haka a hukumance ba a san da zamansu, saboda hakan suna kokarin ganin cewa makarantu fiye da dubu 17 na kasar sun samu rijista, doin kimanin 700 ne kawai suke da ita.

Sheikh Mustafa Lu ya bayyana cewa,a hajjin da ta gabata ya sun samu samar ganawa da Qadi Asakar wakilin jagoran juyin Islama a hajji, kuma sun ji dadin tattaunawa da ta gudana a tsakaninsu, da nufin kara samun fahimtar juna wajen fadada ayyuka na addini da ci gaban makarantun kur’ani a kasar.

3493965

captcha