Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin yau Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da babban sakataren kungiyar Jihadi Islami ta kasar Palastinu Dakta Ramadhan Abdallah da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyara inda ya bayyana abubuwan da a halin yanzu suke faruwa a matsayin kokarin kasashen yammaci karkashin jagorancin Amurka wajen tabbatar da ikonsu ta hanyar amfani da karfi a kan masu riko da addinin Musulunci, inda ya ce: Gagarumin yakin da ke faruwa a halin yanzu a yankin nan (Gabas ta tsakiya), ci gaban yakin da shekaru 37 din da suka gabata aka kaddamar da shi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Batun Palastinu kuwa shi ne a kan gaba a wannan fito na fito da ake yi. Don haka Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kamar yadda tun daga farko ta dauki goyon bayan Palastinu a matsayin wani nauyi da ke wuyanta, a nan gaba ma za a ci gaba da sauke wannan nauyin.
Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa mahanga da kuma matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batun Palastinu ba wai wata matsaya ce ta wani lokaci kawai ba, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Tun kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a daidai lokacin da ake cikin gwagwarmaya, batun goyon bayan Palastinu da kuma wajibcin fada da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa na daga cikin batutuwan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya sha bayaninsa, haka nan bayan nasarar juyin juya halin Musulunci goyon bayan al'ummar Palastinu suna daga cikin abubuwan da muka fi ba su muhimmnaci. A saboda haka a dabi'ance goyon bayan Palastinu yana daga cikin zatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: juyin juya halin Musulunci na Iran yayi nasara ne a daidai lokacin Amurka take cikin tsananin karfinta a wannan yankin sannan kuma a zahiri komai yana tafiya yadda take so ne, to amma haka juyin juya halin Musulunci ya sanya ruhi da karfin gwiwa cikin zukatan al'ummar musulmi da kuma sauya yanayin da yankin yake ciki.
Haka nan yayin da yake ishara matsin lamba kala-kala na siyasa, farfaganda, tattalin arziki kai hatta ma na harin soji da Iran ta fuskanta duk dai da nufin dunkufar da juyin juya halin Musulunci ko kuma tilasta wa gwamnatin Musulunci yin watsi da siyasarta, Jagoran ya bayyana cewar: Abin da a halin yanzu yake faruwa a yankin nan, a hakikanin gaskiya, ci gaban wannan fito na fito da ke gudana tsakanin Amurka da gwamnatin Musulunci ta Iran.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa babbar manufar gagarumin yakin da kasashen yammaci karkashin jagorancin Amurka suka kaddamar kan sansanin masu riko da Musulunci ita ce neman tabbatar da ikonsu a yankin Gabas ta tsakiya, don haka sai ya ce: Da irin wannan mahangar ya kamata a kalli wannan lamurran da kuma yi musu sharhi, sannan kuma bisa hakan ne lamarin Siriya, Iraki, Labanon da kuma Hizbullah ya shigo cikin wannan gagarumin fito na fiton.
Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada cewar a irin wannan yanayin "goyon baya da ba da kariya ga Palastinu, wata alama ce ta goyon bayan Musulunci, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ma'abota girman kan duniya sun yi iyakacin kokarinsu wajen bayyana wannan fito na fiton a matsayin wani "yaki tsakanin Shi'a da Sunna".
Haka nan yayin da yake ishara da cewa gwamnatin kasar Siriya ba gwamnatin ‘yan Shi'a b ace, Jagoran ya bayyana cewar: Amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan gwamnatin Siriya, don kuwa mutanen da suke fada da ita, a hakikanin gaskiya mutane ne da suke adawa da asalin tushen Musulunci sannan kuma suna son tabbatar da manufofin Amurka da sahyoniyawa ne.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar fada tsakanin Shi'a da Sunna, wani makirci ne na ‘yan mulkin mallaka da kuma Amurka, daga nan sai ya ce: Batu mafi muhimmanci a irin yanayin da yankin nan yake ciki, shi ne kyakkyawar fahimtar sansanoni biyun da suke fagen wannan fito na fiton da kuma fahimtar irin matsayin da suke da shi. Don kuwa matukar ba a fahimci kan iyakokin sansanoni biyun ba, to kuwa mai yiyuwa ne mutum yayi fito na fito da sansanin Musulunci bai sani ba.
Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewar da irin wannan mahangar ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran take ganin Amurka a matsayin babbar abokiyar gabarta sannan haramtacciyar kasar Isra'ila kuma a matsayin wacce take biye mata, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A koda yaushe Iran tana daukar goyon bayan lamarin Palastinu a matsayin wani nauyi da ke wuyanta, don haka za ta ci gaba da sauke wannan nauyin.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin gagarumin takunkumin da Amurka da ‘yan amshin shatanta suka sanya wa Iran tsawon shekarun baya-bayan nan, Jagoran ya bayyana cewar: Babbar manufar wadannan takunkumin, ita ce kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga tafarkin da take kai, to sai dai sun gagara cimma wannan manufa ta su, kuma a nan gaba ma ba za su cimma ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Bisa alkawari na Ubangiji, mu din nan mun yi amanna da cewa lalle mu ne za mu yi nasara a yayin wannan gagarumin fito na fito, kuma ya zuwa yanzu mun yi nasara. Don kuwa makiya suna son ganin bayan Jamhuriyar Musulunci ne, to har ya zuwa yanzu ba wai kawai gwamnatin Musulunci tana nan a raye ba ne, face ma dai a kowace rana sai kara samun ci gaba take yi a bangarori daban-daban.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin babban sakataren kungiyar Jihadi Islami dangane da kokarin da wasu suke yi na kara matsa wa kungiyar Hizbullah ta kasar Lababon lamba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Kungiyar Hizbullah dai ta yi karfin da irin wadannan matsin lambar ba za su iya cutar da it aba. A saboda haka ne a halin yanzu irin damuwa da tsoron kungiyar Hizbullah da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi ya fi na shekarun baya yawa.
Har ila yau kuma yayin da yake jaddada tabbatuwar alkawarin Ubangiji na taimako da kuma nasarar sansanin gaskiya a kan karya, Jagoran ya bayyana cewar: Ko shakka wannan nasarar dai tabbas ce, duk kuwa da cewa ana iya fuskantar matsaloli da wahalhalu. To amma dai Allah ba zai saba alkawarinsa na taimakon wadanda suka taimaki addinin Allah ba.
Tun da fari dai sai da babban sakataren kungiyar Jihadi Islamin, Dakta Ramadhan Abdallah ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake mika godiyarsa dagane da goyon baya da matsayar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take dauka dangane da lamarin Palastinu, ya kuma yi Karin bayani dangane da halin da Zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan suke ciki inda ya bayyana cewar: Duk da ci gaban killace Zirin Gaza da ake yi da kuma yanayi na tsanani da ake ciki, amma mutanen Gazan suna nan daram a kan kafafunsu. Haka nan a Yammacin Kogin Jordan ma, duk da irin amfani da karfi da zaluncin sahyoniyawa, to amma ruhin boren Intifadan sai karuwa yake yi a zukatan matasan Palastinawa.
Haka nan kuma yayin da yake jaddada irin shirin da dakarun gwagwarmaya a Palastinu suke da shi bugu da kari kan irin karfin da suke da shi, Dakta Abdallah ya bayyana cewar: Amurkawa da ‘yan amshin shatansu suna kokarin shafa wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kashin kaji da bakanta ta, da kuma sanya a mance da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila, kamar yadda kuma suke kokari wajen rarraba wannan yankin ta hanyar shigo da yakin Shi'a-Sunna. A saboda haka ne suke ta kara matsin lambar da suke yi wa kungiyar Hizbullah. To amma sakamakon irin fahimtar hakan da kungiyar Jihadi Islami ta yi, don haka tana nan daram a kan tafarkinta na goyon bayan kungiyar Hizbullah da gwagwarmayar tinkarar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.