IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Iran Na Amfana Da Mab’as Wajen Tunkarar Jahiliyyar Da Amurka Ke Jagoranta

22:03 - May 06, 2016
Lambar Labari: 3480385
Bangaren siyasa, Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, jamhuriyar musulunci ta Iran tana daukar darasi daga sha’anin aiki manzo wajen tunkarar jahiliyyar wanann zamani karkashin jagorancin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, A safiyar yau Alhamis (05-05-2016) wacce ta yi daidai da ranar da aka aiko Annabi Muhammad (s.a.w.a) a matsayin Annabi kuma Manzo Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'an gwamnatin kasar Iran, jakadun kasashen musulmi da suke Tehran bugu da kari kan wasu daga cikin iyalan shahidan Iran don nuna farin cikin wannan rana mai albarka.

A jawabin da ya gabatar a yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da ci gaba da wanzuwar tafarkin Ma'aiki (s.a.w.a) ya zo da shi da kuma yanayi na jahiliyya tun daga farkon Musulunci har zuwa yau din nan inda ya bayyana "irin shiriyar da bil'adama suka samu ta hannun Annabi (s.a.w.a) a matsayin daya daga cikin fitattun siffofin tafarkin Ma'aiki (s.a.w.a), sannan "sha'auce-sha'auce da kiyayya da gaba" kuma a matsayin wasu daga cikin fitattun siffofin jahiliyya. Daga nan sai ya ce: A halin yanzu mafi muhimmancin nauyin da ke wuyan al'ummar musulmi shi ne fada da yanayi na jahiliyya wanda Amurka take jagoranta. Don haka Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na ja-gaban wannan yanayi na shiriyar da Ma'aiki ya zo da shi, wanda kuma marigayi Imam Khumaini (r.a), ya share fagen samar da shi (a wannan zamanin) za ta ci gaba da tafiya a bisa wannan tafarki da take kai ba tare da tsoron duk wani karfi na duniya ba.

Haka nan kuma yayin da yake taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar aiko Ma'aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske dangane da ma'anar aiko Ma'aiki (s.a.w.a) inda ya ce: Ranar aiko Ma'aiki, wata ranar idi ce ta motsarwa, sannan kuma rana ce ta komawa ga tafarki na Ubangiji da rayuwa tare da amfani da hankali, ‘yanci, adalci da kuma bautar Allah. Don kuwa aikin Manzannin Ubangiji shi ne shiriyar da mutane zuwa ga tsarkin ruhi da aiki karkashin koyarwa da umurni na Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma kadaita Shi.

Har ila yau yayin da kuma ya ke ishara da bukatun da bil'adama suke da ita ga koyarwar sakon Musulunci, Jagoran ya bayyana tafarkin jahiliyya a matsayin kishiryar wannan tafarki na sakon Musulunci yana mai cewa: Tafarkin jahiliyya dai ba wai ya takaita da zamanin Manzon Allah (s.a.w.a) kawai ba ne, face dai wani tafarki ne da ya ci gaba da wanzuwa da kishiyartar tafarkin shiriya wanda Annabawa suka zo da shi, wanda kuma a halin yanzu yana ci gaba da bayyanar da kansa ta hanyar amfani da ilimi da fasaha a salo mabambanta.

Haka nan kuma yayin da yake kara jaddada cewa sha'awa, kiyayya da son zuciya wasu fitattun siffofi na asali ne na wannan tafarki na jahiliyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A koda yaushe sakamakon ayyukan wannan tafarki na jahiliyyan ya kasance shi ne wahala, bala'i da kaskantar da bil'adama da kuma zubar da jinin miliyoyin mutane, kwashe musu dukiyoyinsu da kuma yada fasadi a bayan kasar, wanda babban misalin hakan su ne yakukuwan duniya guda biyu da suka faru a baya.

Har ila yau yayin da yake ishara da cewa samuwar wadannan yanayi guda biyu (shiriyar da Annabi ya zo da ita da kuma tsarin jahiliyya) hatta a yanayi na daidaiku, zamantakewa da kuma fage na kasa da kasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Idan da a ce dabi'u da halayen manyan kasashen duniya a fagen kasa da kasa sun kasance karkashin inuwar koyarwar Annabawa ne, to da kuwa duniya ta zamanto wani abu ne na daban. Amma idan har suka kasance karkashin inuwar son zuciya, neman tabbatar da karfi da mulkinsu da kuma haifar da fitinu, to kuwa duniya za ta kasance wani abu ne na daban.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokarin tabbatar da al'ummomi karkashin mulkin mallaka a matsayin daya daga cikin bayyanannun misalan ayyukan ma'abota riko da tafarkin jahiliyya, daga nan sai ya ce: Fitunu da yake yaken da a halin yanzu suke faruwa a yammacin Asiya, dukkanin hakan sakamako ne na ayyukan jahiliyya da Shaidan.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana tafarkin sahyoniyawa masu juya duniya a halin yanzu a matsayin daya daga cikin fitattun misalan wannan tsari na shaidan da ke iko a duniya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Halin da duniya take ciki a halin yanzu sakamako ne na mulkin cibiyoyin jari hujja ta sahyoniyawan duniya wadanda hatta a kan gwamnatoci irin su Amurka suna da iko da kuma juya su yadda suke so, ta yadda hatta nasara da mulkin jam'iyyun siyasa a wadannan kasashen ya damfara ne da irin biyayya da goyon bayan da suke ba wa wadannan sahyoniyawan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana yunkurin fada da wannan tasiri na sahyoniyawa a matsayin tushen gagarumin yunkurin al'ummar musulmi da na Iran da kuma farkawa ta Musulunci da aka samu a kasashen musulmi inda ya ce: A saboda haka ne a halin yanzu Amurka ta mayar da kiyayya da kuma shafa kashin kaji wa Musulunci, Iran da kuma Shi'anci a matsayin babbar siyasarta da kuma gwamnatoci ‘yan amshin shatanta.

Jagoran ya bayyana irin farkawa da sanin ya kamata da al'ummar Iran da sauran al'ummomin musulmi na duniya suke nunawa wajen tinkara mulkin mallakan masu tinkaho da karfi na duniya a matsayin babban dalilin fushi da kiyayyar da suke nunawa wa wadannan al'ummomin. Don haka sai ya ce: Saboda adawar da Iran take nunawa bakar siyasar Amurka a yankin nan ne ya sanya suke mata barazana da takunkumi, don kuwa suna daukar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin babbar kafar ungulu ga siyasarsu ta mulkin mallaka a yankin nan.

Haka nan yayin da yake bayyana girman kai da dagutanci a matsayin sakamakon ikon masu karfi irin na jahiliyya da shaidanci a duniya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Masu riko da tafarkin jahiliyya da dagutanci su ne ummul aba'isin mutuwar dubun dubatan mutane a Hiroshima sakamakon amfani da makamin nukiliya da suka yi, to amma duk da haka, bayan shekaru aru-aru ba a shirye suke su nemi gafarar wadannan mutanen ba. Haka nan kuma suna ci gaba da ruguza kasashen Iraki da Afghanistan da sauran kasashe amma ba a shirye suke su dawo cikin hankalinsu ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kaddamar da yaki da kai harin soji a kan wata kasa ba, to amma da babbar murya ta sanar da matsaya da kuma mahangarta, sannan kuma a nan gaba ma za ta ci gaba da yin hakan.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganar marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke cewa "Musuluncin da aka bar shi a baya" tare da "Musulunci samfurin Amurka" sun hada hannu waje guda don yakar "Hakikanin Musuluncin da Annabi Muhammadu ya zo da shi", Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A halin yanzu kasashen yammaci suna nan suna ci gaba da goyon bayan lalatattun kungiyoyin wadanda suke fakewa da sunan Musulunci suna aikata mafi munin ta'addanci a bayan kasa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Kasashen yammaci a zahiri wai sun kafa hadin gwiwan fada da kungiyar Da'esh, to amma a hakikanin gaskiya su ne suke taimako da goyon bayan wannan kungiyar. A kafafen watsa labaransu suna kiransu da sunan "gwamnatin Musulunci" don dai sun cimma manufarsu ta bakanta sunan Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin ci gaba da bayyanar kungiyoyi na yunkuri na Musulunci duk kuwa da ci gaba da kokarin bakanta sunan Musuluncin da kasashen yammacin suke yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Yunkuri Musulunci wanda ya sake samun karfi bayan kafa gwamnatin Musulunci a kasar Iran, zai ci gaba kuma a hakikanin gaskiya ma shi zai yi nasara.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada muhimmancin dogaro da Allah Madaukakin Sarki da kuma rashin tsorata da makirce-makircen makiya, Jagoran ya bayyana cewar: A halin yanzu dukkanin al'ummar musulmi kama daga mutane, masana, jami'ai da sauran masu fadi a ji suna da wani nauyi a wuyansu, wanda matukar suka aikata hakan, to kuwa za su sami lada da sakamako na Ubangiji. Sannan duk wanda ya ki sauke nauyin da ke wuyansa, to kuwa yunkurin Musulunci ba zai tsaya ba, zai ci gaba da tafiyarsa. Don kuwa taimakon Allah ga Musulunci da musulmi wani abu ne wanda babu kokwanto cikinsa.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda ya bayyana ranar aiko Ma'aiki a matsayin wata rana ta rahama ga dukkanin bil'adama. Daga nan sai ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ba wai kawai ga musulmi ba, face dai ga dukkanin bil'adama ya kasance wata alama ce ta rahama. Don kuwa ya gabatar da tafarkin shiriya ga dukkanin mutane.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da tuhumar Musulunci da wasu suke da ayyukan ta'addanci da rashin tausayi kuwa, shugaba Ruhani ya bayyana cewar: Mutanen da a halin yanzu bisa zalunci suka kaddamar da siyasar kyamar da shafa kashin kaji ga Musulunci, su sake dubi da idon basira kuma bisa adalci ga koyarwar Musulunci, don su dau darasi daga mu'amala da adalcin Manzon Allah (s.a.w.a) a yayin mu'amalarsa da mushirikai da kafirai.

Sheikh Ruhani ya ci gaba da cewa: A bangare guda masu kiyayya da Musulunci a kasashen yammaci wadanda shekaru aru-aru kenan suke yada bakar farfaganda a kan Musulunci, sannan a daya bangaren kuma jahilan mabiya da ‘yan amshin shatan kasashen yammaci, danjumma da danjummai ne a fagen cutar da Musulunci.

Don haka sai shugaban kasar ta Iran ya gabatar da tambayar cewa su wane ne suka shigo da ayyukan ta'addanci da rashin tsaro yankin nan da kuma kafa wata haramtacciyar gwamnati a yankin nan tsawon shekaru 70 din da suka gabata? Daga nan sai ya ce: haramtacciyar kasar Isra'ila ‘yar fashin Qudus ita ce tushen mafi yawan ayyukan ta'addanci, rashin tsaro da kuma yakukuwan da suke faruwa a yankin nan.

Haka nan kuma yayin da yake magana dangane da mamaye kasar Afghanistan da kuma yakin da aka kaddamar a kan kasar Iraki sannan da kuma rashin tsaron da aka haifar a yankin gabas ta tsakiya, shugaba Ruhani ya bayyana cewar: Sahyoniyawa da Amurkawa su ne ummul aba'isin dukkanin wadannan wuce gona da irin.

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa manufar gwamnatin Musulunci ta Iran ita ce tabbatar da sulhu da tsaro a duk fadin duniya, don haka sai ya ce: Yaya za mu yi shiru alhali mutanen da suke kiran kansu masu kula da Masjid al-Haram suna ci gaba da ruwan bama-bamai a kan al'ummar kasar Yemen?

Shugaba Ruhani ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana alfahari da cewa, bisa shiryarwa da umurnin Jagoran juyin juya halin Musulunci, tana goyon bayan wadanda aka zalunta, kuma za ta ci gaba da yin haka. Sannan kuma a duk inda ya zama wajibi ta taimaki wanda aka zalunta, lalle za ta yi hakan karkashin jagorancin babban kwamandan dakarun Iran kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci.

3495199

captcha