Haka nan kuma yayin da yake ishara da muhimman lamurran da suka faru cikin watannin da suka gabata, da suka hada da bukukuwan ranakun tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci, zabubbukan ‘yan majalisar shawarar Musulunci da ta kwararru da aka gudanar da kuma sanya ido kan tituna da manyan hanyoyi don kiyaye hatsura yayin bukukuwan sabuwar shekara, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana godiya da kuma jinjinawarsa ga kwamandoji da jami'an ‘yan sanda da kuma ministan cikin gida saboda namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro a duk fadin kasar Iran.
Ayatullah Khamenei ya ce duk da cewa an samu raguwar yawan hatsura a kan tituna, to amma har ya zuwa yanzu ana fuskantar matsalar yawan hatsura. A saboda haka yana da kyau rundunar ‘yan sanda da sauran cibiyoyin da abin ya shafa su kara himma wajen ci gaba da rage yawan hatsurran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tsaro a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci wanda matukar babu tsaro to kuwa rayuwar yau da kullum ta al'umma da sauran ayyuka na ilimi, tattalin arziki da gudanarwa na kasa ba za su yiyu ba, don haka sai ya ce: Ko shakka babu tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai da aka sa a gaba, ba za ta yiyu ba matukar babu tsaro.
Ayatullah Khamenei ya bayyana binciko musabbabin rashin tsaro da jami'an sanda da sauran cibiyoyin da abin ya shafa za su gudanar a matsayin wani lamari mai matukar muhimmnaci. Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin taimakawa ‘yan sandan a wannan fagen, Jagoran ya bayyana cewar: Samuwar karfin gwiwa da azamar gudanar da aiki a tattare da kwamandoji da manyan jami'an rundunar ‘yan sanda da kuma irin aiki tukuru da kuma girmamawar da ministan cikin gida yake yi wa jami'an ‘yan sanda, wata dama ce abar amfanuwa da ita wajen isa ga manufar da aka sanya a gaba.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin taimakon ‘yan sanda daga bangaren gwamnati don ciyar da ayyukan ‘yan sandan gaba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin rundunar ‘yan sanda da sauran al'umma, Jagoran ya bayyana tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jami'an ‘yan sandan a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske yana mai cewa: Lafiyar tunani, aiki da kyawawan halaye a tsakanin jami'an ‘yan sandan, wani lamari ne da zai kara karfafa irin alakar da ke tsakanin ‘yan sandan da sauran al'umma.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin kasantuwar ‘yan sandan a dukkanin fadin kasar Iran da nufin tabbatar da tsaron dukkanin fadin kasar cikin kuwa har da birane da kauyuka.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan batun tabbatar da kyawawan halaye a tsakanin al'umma a matsayin wani lamari mai muhimmanci wanda kuma mutane suke fatan ganin an tababtar da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an ‘yan sandan da su ba da himma wajen ganin an tabbatar da hakan yana mai cewa: shaye-shaye, ashararanci da makamantan haka, wasu lamurra ne da suke barazana ga zaman lafiyan al'umma. A saboda haka wajibi ne a yi amfani da kwarewar masana wajen fada da hakan da kuma tsara tsarurrukan da suka kamata.
Ayatullah Khamenei ya kirayi jami'an ‘yan sandan da cewa kada su bari farfaganda da kokarin shafa kashin kaji da wasu suke yi musu a lokacin da suke gudanar da ayyukansu na tababtar da tsaro da kyawawan halaye a tsakanin al'umma ya hana su gudanar da ayyukansu. Kamar yadda kuma Jagoran ya kirayi jami'an ‘yan sandan da su nuna rahama da tausayin al'umma yayin gudanar da aikinsu, duk da cewa wajibi ne su tsaya kyam wajen ganin an tabbatar da doka.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin ci gaban da Iran ta samu cikin shekaru 37 din da suka gabata duk kuwa da kafar ungulun makiya a matsayin wani lamari mai kyaun gaske, don haka sai ya ce: Gwamnatin Musulunci ta Iran tare da goyon bayan al'umma ta samu nasarar turbude hancin makiya, kamar yadda kuma makiyan sun gaza a kokarinsu na haifar da rashin tsaro da mummunan fata a tsakanin al'umma, wanda irin ci gaban da Iran take samu shi ne ummul aba'isin din fushin da suke yi.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kirayi dukkanin al'ummar Iran da suka hada da jami'an gwamnati da sauran al'umma zuwa ga hadin kai a tsakaninsu da kuma nesantar rarrabuwan kai wanda makiya suke son ganinsa a kasar Iran.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mika godiya da kuma jinjinawarsa ga iyalan kwamandoji da sauran jami'an sandan saboda irin hakuri da juriyar da suke nunawa.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da babban sufeto janar na ‘yan sandan Iran din Birgediya Janar Ashtari ya gabatar da jawabinsa da kuma yin Karin haske dangane da irin ayyukan da rundunar ‘yan sandan take yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan kasa.