IQNA

Sakon Jagora A Yayin Bude Zaman Majalisa:

Mayar Da Hankali Ga Tattalin Arziki Mai Karfi Da Koyarwar Muslunci Shi Ne Ake Bukata

23:52 - May 31, 2016
Lambar Labari: 3480464
Bangaren siyasa, Ayatollah sayyid Ali Khamenei a cikin sakon da ya aike zuwa ga sabuwar majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, babban abin ake bukata daga gare su a halin yanzu a cikin sari shi ne karfafa tattalin arziki da kuma kara bunkasa koyarwar musulunci.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a cikin wani sako da ya aike wajen bikin rantsar da sabbin ‘yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran karo na goma, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gode wa al'ummar Iran saboda irin gagarumar fitowar da suka yi yayin zaben ‘yan majalisar sannan kuma ya kirayi ‘yan majalisar zuwa ga kokari wajen tabbatar da tattalin arzikin na dogaro da kai da kuma fadada al'adun Musulunci haka nan kuma da nesantar shagaltuwa da abubuwa na kungiyanci da fifita manufofi na kashin kai a kan na al'umma gaba daya; yana mai cewa: Nauyi na juyin juya hali da kuma dokokin kasa da ke wuyanku shi ne ku yi kokari wajen samar da tsayayyiyar majalisar wacce za ta zamanto katanga a gaban kokarin wuce gona da irin ma'abota girman kai sannan kuma mafakar mutane muminai ma'abota riko da juyin juya hali.

Abin da ke biye fassarar sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci wanda Hujjatul Islam wal muslim Muhammadi Golpaygani, shugaban ofishin Jagoran, ya karanto a safiyar yau Asabar (28-05-2016) wajen bikin rantsar da ‘yan majalisar:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina taya al'ummar Iran da kuma ku din nan zababbu wadanda kuka karbi wannan nauyi mai girman gaske na zama ‘yan majalisa murnar fara aikin majalisar shawarar Musulunci karo na goma a watan Sha'aban, wanda wata ne na kusaci da kuma kaskantar da kai a gaban Allah kana kuma wata ne na ranakun farin ciki na addini. Kamar yadda kuma na ke mika godiya ta ga daukacin al'ummar Iran sakamakon wannan gagarumar fitowa da suka yi yayin zaben ‘yan majalisar dokokin. Dukkanin hakan ya samo asali ne daga dacewa ta Ubangiji kana kuma alama ta rahama da tausayawarsa wanda ya samar wa al'umma, kasar Iran da kuma tsarin Musulunci wata garkuwa mai karfin gaske da kuma kariya a gare su. Lalle zuciya da harshe sun gaza wajen gode wa wannan babbar ni'ima.

Al'ummar Iran, ta hanyar wannan gagarumar fitowar da suka yi wajen zaben ‘yan majalisar dokoki, a hakikanin gaskiya sun sake jaddada bai'arsu ce ga tsarin Jamhuriyar Musulunci, sannan kuma sun mayar da martani ga masu bakar aniya a kansu. Irin wannan sadaukarwa ta al'umma, wani lamari ne da ke wajabta wa jami'an gwamnati na dukkan bangarori karin jin nauyin da ke wuyansu da kuma godiya ga ni'ima. A halin yanzu nauyin da ke wuyanmu, mu jami'an gwamnati, ya karu sama da na baya.

Rantsuwar kama aiki, wanda ‘yan majalisar suke yi a ranar farko na fara aikinsu, wanda kuma wata rantsuwa ce ta shari'a da wajibi ne a aiwatar da ita, ta yi bayanin manyan ayyukan ‘yan majalisar yayin gudanar da aikinsu a majalisa. Ku din nan ‘yan'uwa maza da mata masu girma za ku iya sauke wannan nauyi da ke wuyanku - wanda a mafi yawan lokuta shi ne kafa dokoki da kuma sanya ido - ta hanyar amfani da hikima, hangen nesa, ikhlasi da kuma tsoron Allah, sannan kuma ku sami daukaka a wajen Allah da kuma mutane. Ta haka ne za ku iya kiyaye matsayi na musamman da majalisar shawarar Musulunci take da shi, wato "zama kan gaba cikin lamurran gudanar da kasa".

Irin halin rashin tabbas da yankin nan da kuma duniya baki daya suke ciki da kuma irin fitina da rashin tsaron da ‘yan mulkin mallaka da ‘yan amshin shatansu suka haifar, lamari ne da ya sanya kasar Iran cikin wani irin yanayi mai sarkakiyar gaske sama da baya. A saboda haka akwai bukatar hikima da tsayayyiyar azama da aiki tukuru daga wajen dukkanin jami'an gwamnati wajen karfafa kasar nan don tinkarar wannan yanayin. Nauyi na juyin juya hali da kuma doka da ke wuyanku, Ya ku ‘yan majalisa masu girma, shi ne ku yi kokari wajen samar da tsayayyiyar majalisar wacce za ta zamanto katanga a gaban kokarin wuce gona da irin ma'abota girman kai sannan kuma mafaka kana abin dogaron mutane muminai ma'abota riko da juyin juya hali.

Tabbatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai da dukkanin bangarorinsa haka nan da kuma kokari ba kama hannun yaro wajen karfafawa da kuma fadada al'adun Musulunci, wasu nauyi na gaggawa da ake bukatar sauke su ne. Wani nauyin kuma na daban mai muhimmanci a bangarori daban daban shi ne tabbatar da karfi na kasa da tsaro da lamuni daga dukkanin barazana, wanda hakan ne zai lamunce tabbatuwar adalci na zamantakewa, ‘yancin kai da kuma ci gaban kasar nan. Fahimtar wadannan batutuwa suna daga cikin nauyin da ke wuyan ‘yan majalisa wanda kuma kwakwalansu za su iya riskarsu.

Ina kiran ‘yan majalisa masu girma zuwa ga dogaro da Allah da kuma kyautata zato ga alkawarinsa da kuma tsayin daka a bisa mikakken tafarkin Ubangiji, kamar yadda kuma na ke jan kunnen su daga shagaltuwa da batutuwa na kungiyanci da fifita manufofi na kashin kai a kan manufofi na al'umma.

Ya zama wajibi in mika godiya da kuma jinjinawa ta ga ‘yan majalisa ta tara da kuma shugabanta mai kokari da hidima da kuma dukkanin jami'an majalisar, haka nan kuma ga dukkanin jami'an da suka gudanar da zaben ‘yan majalisa na tara da dukkanin bangarorinsa.

Ina jinjinawa marigayi Imaminmu mai girman matsayi (Imam Khumaini) da shahidai da masu sadaukarwa a wannan tafarki. Haka nan kuma ta hanyar mika gaisuwa da kuma sallama ta girmamawa ga mai girma Waliyullahil A'azam (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) ina roka muku dacewa daga wajen Allah Madaukakin Sarki.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Sayyid Ali Khamenei

7, Khordad, 1395.

(27, Mayu, 2016)

3501533

captcha