IQNA

Khalifan Muridiyyah A Senegal:

Ku Isar Da Sakon Gaisuwata Ga Jagoran Iran

23:38 - August 10, 2016
Lambar Labari: 3480696
Bangaren kasa da kasa, khalifan darika muridiyyah a Senegal ya bayar da sakon gaiswa ga jagoran juyin Islama na Iran da shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na dakar.icro.ir cewa, Ainullah Qasqawi jakadan Iran da Sayyid Hassan Ismati shugaban ofishin raya al’adu da kuma Shir Shekar mataimakin jakadancin Iran Senegal, sun ziyarci khalifan darikar Muridiyyah Sheikh Mukhtar Mbaki a garin Tuba da ke tazarar kilo mita 200 daga Dakar.

Jakadaun Iran sun isar da sakon gaisuwa daga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei (DZ) da shugaban kasar Hassan Rauhani ga jagoran darikar Muridiyyah Sheikh Mukhtar Mbaki, kamar yadda suka mika masa sakon gayyata zuwa kasar Iran.

Khalifan Muridiyyyah ya bayyana jin dadinsa maras misiltuwa, kamar yadda kuma ya bayyana ziyarar ta tawagar Iran zuwa gidansa da cewa, ziyara mai matukar girma a gare shi, kuma hakan ya tuna masa da ziyarar Ayatollah Rafsanjani a wasu shekaru masu yawa da suka gabata a lokacin da ya kawo masa ziyara.

Ya kara da cewa nan ba da jimawa zai sanar da wata tawaga ta musamman da za ta kawo ziyara akasar Iran, domin kara karfafa hadin kan al’ummar musulmi.

Haka nan kumatawagar ta gana da Abdulahad magajin garin Tuba, da kuma wasu daga cikin manyan jagororin darikar ta Muridiyyah, kamar yadda kuma suka ziyarci hubbaren Sheikh Amadou Bamba wanda ya assasa darikar Muridiyyah.

Wannan darika dai tana da mabiya a sasa na nahiyar Afirka da kuma kasashen turai, inda suke bin wani tsari na musamman na karfafa ruhi da bautar ubangiji madaukakin sarki, tare da tarbiyantar da rai kan bautar Allah shi kadai.

3521527

captcha