IQNA

Bayan Watsa Sakon Hajji Na Jagora:

Babban Malamin Wabiyawa Ya kafirta Iraniyawa / Martanin Zarif

13:15 - September 08, 2016
Lambar Labari: 3480766
Bangaren kasa da kasa, Abdulaziz Al Seikh babban ma bayar da fatawa ga gidan sarautar wahabiya na Al Saud ya kafirta al’ummar musulmi na Iran.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, bayan fitar da sakon jagoran juyin juya halin Islama Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei babban malamin wahabiyawa na duniya ya kafirta al’ummar musulmi na kasar Iran baki daya.

Ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif yayi kakkausar suka ga kalaman babban muftin kasar Saudiyya na kafirta al'ummar Iran inda ya ce ko shakka babu akidar mafiya yawan al'ummar musulmin duniya ta yi hannun riga da akidar wannan mufti da makamantansa da suka ginu wajen goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na Twitter a matsayin mayar da martani ga muftin kasar SaudiyyaSheikh Abdul Aziz Al ash-Sheikh inda ya ce: "Tabbas Musuluncin al'ummar Iran da na mafiya yawan al'ummar musulmin duniya ya bambanta da akidar wuce gona da iri wacce wannan babban malamin wahabiyyawa da jagororin ta'addanci na Saudiyya suke yadawa".

Kafin hakan dai babban muftin kasar SaudiyyanSheikh Abdul Aziz Al ash-Sheikh ya shaida wa wata jaridar larabci cewa al'ummar Iran dai ba musulmi ba ne a matsayin mayar da martani ga sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aikewa mahajjatan bana.

A cikin sakon nasa dai Ayatullah Ali Khamenei yayi kakkausar suka ga yadda mahukuntanSa'udiyya suke gudanar da sha'anin aikin hajji, kamar yadda kuma ya zargi hukumomin Sa'udiyya da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa dubbban alhazan da suka fito daga kasashe daban-daban na duniyayayin turmutsutsin da ya faru ranar sallar bara a Mina lamarin da da dama suke zargin Saudiyyan da hannu cikin hakan.

A yayin wannan turmutsutsi na Mina din dai mahukuntan Saudiyyan sun yi ikirarin cewa kimanin mutane dari bakwai da sabain ne suka rasa rayukansu alhali jami'an Iran da wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa kimanin mutane dubu hudu da dai bakwai cikinsu kuwa da Iraniyawa dari hudu da sattin suka rasa rayukansu.

3528473


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha