IQNA

Gasar Kur’ani Ta Duniya Karo Na Sha Biyu A Morocco

21:20 - October 14, 2016
Lambar Labari: 3480855
Bangaren kasa da kasa, a cikin wata mai kamawa ne za a bude gasar karatu na tartili da hardar kur’ani gami tajwidi da kuma tafsiri a birnin Kazablanka na kasar Morocco.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na inewsarabia.com cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco ta sanar da cewa, wannan shi ne kari na 12 da za a gudanar da wannan gasa ta sarki Muhammad na shida a kasar.

Bayanin ma’aikatar kula da harkokin addinin ta kasar Morocco ya kara da cewa, taron gasar zai samu halartar makaranta da mahardata daga kasashen larabawa da na msuulmi da ma sauran kasashen duniya.

Bisa ga wannan rahoto za a bude babban zaman taron ne a cikin watan gobe, a babban masallacin Hassan na 2 da ke birnin kazablanka, daya daga cikin manyan biranan kasar.

3537503


captcha