IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa A Lebanon

22:56 - October 19, 2016
Lambar Labari: 3480866
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar shirye-shiryen gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya karo na goma sha tara.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, cibiyar taujih da irshad ce za ta dauki nauyin gudanar da wannan gasa, wadda za ta kunshi bangarori na tilawa da harda da kuma tajwidi gami da tafsiri.

Dukkanin bangarorin gasar dai za su kunshi maza da kuma mata da suke da sha’awar shiga cikin wannan gasa.

Beirut, Nabtiyya, Sur, Ba’alabak da Hermil su ne yankuna biyar na kasar da za a gudanar da wannan gasa, wadda za ta kunshi mutane masu shekaru daban-daban daga 15 har zuwa 45 da suke da sha’awa.

Haka nan kuma an bayyana cewa bangaren harda zai kunshi izihi 5, ko 10, 20, da kuma 30, kamar yadda tafsiri zai shafi wasu bangarori da ya hada da surat ahzab, kamar yadda cibiyar taujih da irshad ta sanar a cikin littafin da ta buga kan gasar da kuma Karin bayani kan yadda za a gudanar da ita.

3539140


captcha