IQNA

An Tarjama Littafin Bayanan Jagora Kan Gwagwarmayar Imam Hussain

22:49 - October 24, 2016
Lambar Labari: 3480880
Bangaren kasa da kasa, an tarjama wani littafi wanda ya kunshi bayanan jagora Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khameni (DZ)a cikin harshen larabaci a Iraki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Baghdad.icro cewa, wannan littafi ya kunshi shafuka 165 nea cikin asalin littafin na farisanci, wanda aka buga kwafi dubu 3 bayan tarjamarsa.

Littafin dai ya kunshi bayanan jagora ne kan muhimamn abubuwan da gwagwartmayar ashura ke koyar da musulmi, da kuma abubuwan da ya kamata a dauke su domin su zama darasia cikin rayuwa baki daga abin da wannan imami mai tsarki tare da sahabbansa suka yi, da kuma barin abubuwa da basu da asali ko kuma suke kauda jama’a daga manufar ashura.

An gabatar da wannan littafi nea lokacin gudanar da taron na fadakar al’ummar musulmi karo na tara a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

A yayin wannan taro dai an samu halartar manyan mutane da suka hada da malamai, da kuma jami’an gwamnati, kamar yadda masana ma ba a bar su a baya ba wajen gudanar da wannan taro, inda aka gabatar da muhimman makaloli guda 9 da aka yi bahasi kansu.

Babbar manufar wannan taro dai itce kara fadakar da al’umma kan halin da ake ciki na makircin da makiya suke kulla ma musulmi domin rusa kasashensu, musamman ma larabawa, wadada abin ban takaici wasu daga cikin gwamnatocinsu da sarakunasu suna a sahun gaba wajen aiwatar da wannan bakar manufa ta makiya musulunci.

3540424

captcha