IQNA

Daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da rayuwarsa domin neman yardar Allah

Barkanku Da Shiga Sabon Watan Na Rabi’ul Awwal

Daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da rayuwarsa domin neman yardar Allah

"Daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da rayuwarsa domin neman yardar Allah ...” (surat baqarah / 207)

Wannan aya mai albarka ta safka ne kan sha’anin Ali Amirul muminin (AS) a farkon watan Rabi’ul Awwal.

Daren da manzon Allah (SAW) ya yi hijira daga Makka zuwa Madinah domin kauce wa sharrin kafirai.

Imam Ali (AS) gwarzon da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, ya kwanta akan gadon manzon Allah (SA) domin manzon Allah ya samu damar ficewa saboda ya tsira da ransa, ana kiran wannan dare da daren Mubit.

Ghazali ya kawo a cikin littafin Ihya’u l ulum cewa:

A daren da Imam Ali (AS) ya kwanta kan gadon manzon Allah (SAW) an da Jibril da Mika’il, a matsayinku na ‘yan uwa biyu, an sanya rayuwar daya daga cikinku tafi tsawo a kan rayuwar daya, wane ne daga cikinku ke son rayuwa mafi tsawo?

Sai dukkaninsu biyu suka zabi rayuwa mafi tsawo, sai aka ce da su, ku duba kasa ku gani a kasa, yadda Aliyu ya sadaukantar da rayuwarsa domin dan wansa Muhammad ya tsira daga sharrin kafirai, ya kwanta a kan gadonsa domin duk abin da zai samu dan uwansa shi ya same maimakon dan uwansa Muhammad (SAW) ku safka ku kare shi daga sharrin kafirai.

Sai suk safka, Jibril ya tsaya a kan Amirul muminin Mika’il kuma ya tsaya a kan kafafunsa, sna cewa muna taya ka murna ya dan Abu Talib, Allah yana yabonka a cikin tarin mala’iku.

A nan wannan aya "Daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da rayuwarsa domin neman yardar Allah ...” ta safka.

Ihya’u l ulum – Ghazali, littafi na 7, bahasin sadaukantar da rai.

Download: Image Size: