IQNA

Azhar Ta Bukaci A Kawo karshen Zaluncin Da Ake Yi kan Musulmi A Myanmar

23:40 - December 19, 2016
Lambar Labari: 3481049
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar da ke Masar ya yi da a kawo karshen zaluncin da ake yi kan musulmi a kasar Myanmar.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Jaridar Aldastur cewa, a lokacin da Ahmad Tayyib yake ganawa da jakadan kasar Myanmar a Masar a jiya Mini Luin ya bayyana cewa, yana kira ga mahukuntan Mayanmar da su kawo karshen kisan gillar da ake yi wa musulmi marassa rinjaye a kasar.

Ya ce Azhar ta damu matuka dangane da halin da musulmin Myanmar suke ciki, kuma a shirye take t abayar da dukkanin taimakon da ake bukata domin ganin an sasanta tsakanin mahukuntan Myanmar da musulmi da ake zalunta a kasar.

Shi ma a nasa bangaren jakadan Myanmar a Masar Mini Luin ya bayyana cewa, zai isar da sakon Azhar ga mahukuntan kasarsa, kuma ya yi kokarin wanke gwantain kasar tasa dangane da irin tuhumce-tuhumcen da take fuskanta, na cewa tana da hannu kai a kisan giyashin da ake yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingya, inda ya ce rikici ne kawai tsakanin msuulmi da kuma mabiya addinai na yankin.

Wannan furuci na jakadan Myanmar a Masar ya yi hannun riga da abin da yake wakana a kasa, wanda dukanin al’ummomin duniya suke gani na kisan gilla da sojojin kasar ta Myanmar suke yi wa musulmi tare da kone musu gidaje da dukiyoyi da kuma mayar da su yan gudub hijira, baya ga fyade da ake yi wa matansu.

Yanzu haka dai kasashen yankin gabashin nahiyar asia suna gudanar da tattaunawa atsakaninsu domin sanin matakan da za a dauka kan wannan batu, sakamakon matsin lamabra da suke sha daga sauran alummomi na duniya.

3555004


captcha