Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Jaridar Independent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa,a kowace shekara musulmin kasar Birtaniya sukan bayar da kyautuka ga kiristoci marassa galihu, amma a wannan shekara lamarin ya kara bunkasa fiye da kowane lokaci a baya, inda a cikin birnin London, daruruwan msuulmi ne suke zagaya a kowane sako dauke da kayayyakin abinci, inda suke bayarwa ga marassa galihu, gami da wasu kyautuka na musamman na bikin kirsimati.
Kwamitin babban masallacin yankin White Chepel da ke gabashin birnin London ne ya dauki nauyin shirya wannan aiki na bayar da taimako gami kyutukan kirsimati ga kiristoci marassa a karfi.
Delawar Khan wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin ya bayyana cewa, sun kudiri aniyar gudanar da wannan aiki ne domin isar da sakon zaman lafiya da tausayawa dan adam da taimakonsa, kamar yadda addinin muslunci ya koyar da musulmi.
Ya ce ko shakka babu wasu da dama a kasar suna mummunar fahimta kan musulmi, amma ta hanyar gudanar da irin wadannan ayyuka na alkhairi, jamar kasar za su gane cewa musulmi ba 'yan ta'adda ba ne, kuma su masu son zaman lafiya da kyauatata rayuwar zamantakewa ne da sauran al'ummomi mabiya wasu addinai.
Shi ma a nasa bangaren shugaban cocin gabashin birnin London ya mika godiyarsa ga musulmi dangane da irin taimakon da suke baiwa kiristoci marassa galihu a kasar, wanda acewarsa hakan ya kara tabbatar da cewa musulmi da kirista dukkaninsu suna bin addinai ne guda biyu da aka safkar daga sama, domin kuwa wadannan addinan guda biyu ne suka yi umarni da ayyukan alkhairi da taimakon marassa galihu daga cikin 'yan adam.