IQNA

An Fitar Da Wasu Musulmi Biyu Daga Cikin Jirgin Amurka

20:12 - December 22, 2016
Lambar Labari: 3481060
Bangaren kasa da kasa, kamfanin Delta Air Lines ya fitar da wasu musulmi biyu fasijoji daga cikin jirginsa.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na villagevoice cewa, Adam Saleh wani matashi musulmi dan kasar Amurka a zantawarsa da jaridar Guardian ya bayyana cewa, sakamakon maganar da ya yi da larabci tare da matarsa a cikin jirgin wani fasinja ya nuna damuwarsa.

Ya ce ganin haka ya sanya ya yanke wayar domin kada mutane su shiga cikin damuwa, amma wannan fasinjan ya tsaya kai da fata dole sai an kore shi daga jiorgin, iodan kuma bah aka shi zai fita.

Ma’aikatan jirgin sun tuntubi ‘yan sanda domin jin ko akwai wani abu da suke da shakku a kansa, sun tabbatar da cewa mutanen ad suke ciikin jirgin babu wani da suke da rahoton wata matsala a kansa, amma duk da haka ma’aikatan jirgin suka fitar da su tare da abokoinsa, wanda shi ma musulmi ne balarabe amma dan kasar Amurka.

Kamfanin jiragen Delta Air Lines ya ce ya fitar da wadannan musulmi biyu ne daga cikin jirgin fasinja, saboda was fasinjoji kimanin 20 sun nuna rashin amincewa da daukarsu.

Akwanakin baya ma wannan jirgi ya dauki wani fasinja msuulmi tare da matarsa daga kasar Faransa zuwa jahar Ohio ta Amurka, amma an fitar da su daga jirgin saboda sun ambaci sunan Allah.

3555788


captcha