IQNA

Sayyid Nasrullah: Tuhumar Musulunci Da Ta'addanci Makirci Ne

22:42 - December 23, 2016
Lambar Labari: 3481061
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah, ya bayyana cewa kiran kungiyoyin 'yan ta'adda da sunaye masu kama da muslunci irin su daular muslunci ko ta'addancin mulsunci da kalmamomi masu kama da haka, duk yunkuri ne na yakar muslunci da rusa shi a fakaice.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a yammain yau Juma'a a lokacin da yake gabatar da wani jawabi ga dubban daliban jami'a a birnin Beirut, inda ba a karnonin baya-bayan nan ba taba samun wani lokaci da aka bakanta sunan muslunci da fuskarsa a idon duniya kamar wannan lokacin ba, inda ake amfani da sunan muslucni da sunnar manzon Allah (SAW) wajen aikata ayyuka na ta'addanci a kan musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Dangane da tsarkake birnin Aleppo (Halab) na kasar Syria daga 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyyah kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan a matsayin babban koma ga dukkanin aikin da kasashe masu daukar nauyin ta'addanci a Syria suka yi na tsawo shekaru fiye da 5, kuma hakan ya karya lagon 'yan ta'adda da wadanda suka kirkiro su kuma suke daukar nauyinsu, inda ya yi ishara da cewa, masu daukar nayin ta'addanci sun koma a kafafensu na yada labarai, irin su tashar Alarabiyya mallakin gwamnatin Saudiyya, da Aljazeera mallakin gwamnatin Qatar, da kuma CNN ta Amurka da sauran makamantansu, inda suke ta kokarin nuna wa duniya cewa fatattakar 'yan ta'adda da aka yi a Aleppo kisan fararen hula ne ake yi, inda har sukan hada hotunan kananan yara da mata da Saudiyya ke kashe a Yemen a matsayin hotunan Aleppo, wanda hakan ke nuna kidimar da suke ciki sakamakon korar 'yan ta'adda da suke marawa baya.

Haka nan kuma ya jinjina wa al'ummar Syria da gwamnatin kasar gami da dakaruun kasar sakamakon tsayin dakan da suka yi wajen ganin sun kare kasarsu, ya ce; da ba don tsayin dakan al'umar Syria da sojojin kasar ba, kawayen Syria masu taimaka mata da ba su iya yin komai a kasar ba. Haka nan kuma ya bayyana cewa 'yantar da Aleppo daga 'yan ta'adda ba ya na nufin kawo karshen rikicn Syria ba ne, amma dai hakan wani babban kayi ne 'yan ta'adda da masu mara musu baya suka sha.

Haka nan kuma ya ja hankulan musulmi da su zama cikin fadaka dangane da hadarin da ke tatatre da akidar wahabiyanci na kafirta musulmi, wanda shi ne tushen dukkanin ta'addacin da ake aikatawa da sunan addinin muslucni a duniya, kan hadarin wannan akida ya bayar da misalin bawahabiyan da ya tura 'ya;'yansa mata guda biyu 'yan shekaru bakwai da takwas suka tayar da bama-bamaia cikin birnin Damascu tare da kashe musulmi da dama, duk da sunan jihadi a tafarkin sunnar manzo, wanda hakan ya yi hannun riga da sunnar manzon Allah da kyawawan dabi'unsa na rahma da tausayi da jin kai ga dukkanin bil adama, wanda kuma wannan shi ne hakikanin koyarwar akidar wahabiyyah takfiriyyah.

A bangare guda kuma ya gargadi kasar Jordan kan ta sake yin nazari danagne da taimakon 'yan ta'adda da take yia Syria saboda wasu 'yan kudade wasu sarakunan larabawa suke bata, inda ya ce abin da yab faru a cikin wannan mako a Jordan na kisan jami'an tsaro da 'yan ta'addan da gwamnatin kasar ke marawa baya suka yi, ya isa ya zama darasi.

Kamar yadda kuma ya yi gargadi mai kama da hakan ga gwamnatin Turkiya, wadda ya ce ita ce ta baiwa 'yan ta'adda taimako a Syria da Iraki fiye da kowace kasa a duniya, domin kuwa hatta kasashen turai da na larabawa da ke taimakon 'yan ta'adda suna bi ta hannun Turkiya ne, amma duk da haka a cikin kwanaki biyu da suka gabata 'yan ta'addab ISIS sun kashe sojojin Turkiya 18, tare da kona wasu da wuta da ransu, tare da yin garkuwa da wasu masu yawa.

Haka nan kuma ya yi Allawadai da kisan kiyashen da masarautar Saudiyya ke kan kananan yara da mata a kullum rana ta Allah a kasar Yemen a idon dukkanin al'ummaomin duniya, ba tare da wani ya ce uffan ba, wanda hakan ke kara tabbatar da munafunci irin na kasashe masu babatu wajen kare hakkin 'yan adam, inda suke babatu kan korar ta'adda daga Aleppo amma sun gum da bakinsu kan kisan fararen hula a Yemen.

3555959


captcha